A kwanakin baya, an dawo da babi na 2 da na 3 masu taken “Wu Xing Ling” da “Gong Shou Zhan” na Rubutun siliki na Zidanku, wato kayan tarihi mai muhimmanci na kasar Sin, ta hanyar hadin gwiwa kan kayan tarihi tsakanin Sin da Amurka. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Litinin cewa, wannan misali ne na yadda Sin ta cimma nasarar neman dawowar kayan tarihi da suka bata tun a zamanin da, kana nasara ce da Sin ta samu wajen yin kira ga yin shawarwari da hadin gwiwa don sa kaimi ga tabbatar da dawo da kayan tarihin da suka bace.
Mao Ning ta bayyana cewa, Rubutun siliki na Zidanku, shi ne irinsa daya kacal na lokacin yake-yake a zamanin da na kasar Sin da aka gano, kana ya zuwa yanzu, shi ne rubutun siliki mafi dadewa a kasar Sin da aka gano, kuma rubutu ne na bayani na farko a kasar Sin, don haka yana da muhimmanci sosai. Ta ce Sin ta yabawa kungiyar Smithsonian Institution da gidan adana kayan tarihi na nuna fasaha na Asiya na kasar Amurka da sauran hukumomin raya al’adu da kula da kayan tarihi da suka yi kokari kan wannan batu. A cewarta, wannan lamari ya shaida cewa, idan Sin da Amurka sun yi hadin gwiwa bisa tushen daidaito da girmama juna, to za a samu moriyar juna. Sin tana fatan bangarorin biyu za su kara mu’amala da hadin gwiwa don sada zumunta a tsakanin jama’arsu da kuma sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu mai dorewa yadda ya kamata. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp