Kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen ba da gudummawa ga ci gaban Afirka ta hanyar ginawa da gyara muhimman ababen more rayuwa kamar madatsun ruwa da tituna da asibitoci, wadanda suka karfafa dunkulewar yankin, da habaka cinikayya da masana’antu. Don haka, yawancin kasashen Afirka suna daraja hadin gwiwarsu da kasar Sin, saboda tana goyon bayan manufofinsu na ci gaba. A fannin kiwon lafiya, tallafin jinya na kasar Sin ya inganta samun damammaki da walwala ga yawancin kasashen Afirka. Haka ma, shirye-shiryen horar da ilimi da fasaha, irin su tallafin karatu da kafa cibiyoyin Confucius da na Luban da dai sauransu sun inganta jarin dan Adam tare da tallafawa ayyukan zamanantar da Afirka.
Hadin gwiwar Sin da Afirka ta haifar da nasarori mara misaltuwa wandanda suka rusa ikirarin kafafen yada labaran kasashen yammacin duniya na cewa kasar Sin tana “mallakar” Afirka. Hasali ma, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ya zama misalin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa bisa daidaito ba tare da mamaya ba, wadda ke nuna sabon salo na sahihin tsarin hadin gwiwar dake tsakanin kasashen duniya, wadda kuma ta ginu bisa mutunta juna da samun moriyar juna. A gun taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ko FOCAC na shekarar 2024 da za a gudanar daga ranar 4 zuwa ta 6 ga wannan wata, shugabannin bangarorin biyu za su yi musayar ra’ayoyinsu da yin hadin gwiwa bisa taken “Hada hannu don ciyar da zamanantarwa gaba, da gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya”.
Mu dawo kan batun “Mallaka” wato “Colonialism” a Turance, wannan kalma ce da ake yawan samu a cikin litattafan tarihi, wadda akasari ke da alaka da tsarin mulkin mallakar kasashen yamma, wadda a halin yanzu wasu kafafen yada labarai da ‘yan siyasa na kasashen yamma suke lakabtawa ayyukan kasar Sin a Afirka cikin shekarun nan. Tambayar ita ce, me ya sa kasashen yamma ke zargin kasar Sin da yin mulkin mallaka a Afirka? Shugaban kasar Burundi Ndayishimiye ya ba da amsar wannan tambayar, inda ya ce: “Lokacin da ‘yan mulkin mallaka da suka yi mulkin mallaka suka ga yadda kasar Sin ke kara karfi da kuma sha’awarta na yin hadin gwiwa da kasashen Afirka, dole tunanin mulkin mallakar da suka yi wa kasashen Afirka ya dawo musu”. Dole ne mu fahimci cewa tsarguwa ce kawai ke sanya kasashen yamma rura wutar kiyayya da adawa da kasar Sin. (Mohammed Yahaya)