ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin Gwiwa Hanya Ce Madaidaiciya Wajen Kiyaye Tsaron Shiyya

by CGTN Hausa and Sulaiman
6 months ago
Tsaro

Daga ranar 30 ga watan Mayu zuwa ranar 1 ga watan Yuni, an gudanar da taron tattaunawa na Shangri-La karo na 22 a kasar Singapore. Taron tattaunawar, wani nau’in taro ne da ya samar da dandali na karfafa mu’amala da fahimtar juna ta hanyar tattaunawa, to sai dai kasar Amurka ta mai da taron a matsayin fage na shafa wa kasar Sin bakin fenti da ma gurgunta fahimtar sassa daban daban game da hakikanin gaskiyar lamurra. A wajen taron, sakataren tsaron kasar Amurka Pete Hegseth ya yi kalaman da ba su dace ba game da kasar Sin, inda ya yada karairaiyi na wai “barazanar kasar Sin ta fannin soja”, don neman yayata manufarta ta Indo-Pasifik a matsayin wani mataki na tilas da ya dace a dauka wajen tinkarar “barazana daga kasar Sin”.

Sai dai tarihi madubi ne da ya shaida ainihin burin da Amurka ke neman cimmawa. Idan mun yi nazari a kan tarihin yadda kasar Amurka ta kafa mulkin mallaka a kasar Philippines bayan yakin da ta yi tare da kasar Spaniya a shekarar 1898, za a ga cewa ta fake ne da sunan wai “kiyaye tsaron shiyyar”. Haka nan, idan mun yi la’akari da tsarin ayyukan soja da aka kafa sakamakon yarjejeniyar hadin gwiwa da tsaro da Amurka da Japan suka cimma bayan yakin duniya na biyu, har ma da dimbin sansanonin soja da ta kafa a yankin Asiya da tekun Pasifik, za a ga shi ma har yanzu Amurka na fakewa da sunan wai kariya. Lallai Amurka ta saba fakewa da batun tsaro wajen kara karfin sojanta a duniya, sai dai a bisa akasin abin da take fada na wai “barazana daga kasar Sin”, tun bayan da kasar Sin ta gabatar da ka’idoji biyar na zaman tare cikin lumana a wajen taron Bandung yau shekaru 70 da suka wuce, kasar ta Sin ta kwance damarar sojoji kimanin miliyan, kuma ta fi daukar nauyin ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, kana kullum tana dukufa a kan samar da ci gaba a sassan duniya don sa kaimin tabbatar da tsaro, a kokarin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma ci gaba a sassan duniya.

Idan mun yi la’akari da hakikanin yanayin da muke ciki yanzu, za mu gano cewa, abin da Amurka take fada na wai “yankin Indo-Pasifik mai ‘yanci”, babakere da nuna fin karfi ne a zahiri. Yadda jiragen sojan Amurka suka sha yin zirga-zirga a tekun kudancin kasar Sin mataki ne na tsokana wadda yarjejeniyar MDD game da dokar teku ta hana, sannan duk da haka, ta bayyana rashin gamsuwarta game da “’yancin zirga-zirga” a yankin, sai dai ta manta da mene ne yake samar da tsaro, wato tsaro ga kowa a maimakon tsaro ga wata kasa kadai shi ne abin da zai iya tabbatar da tsaro, kuma ba zai yiwu ba wata kasa ta tabbatar da tsaron kanta bisa ga lalata tsaron sauran kasashe ba. Kasar Sin a nata bangaren, ta dukufa a kan gina al’umma mai makoma ta bai-daya ta fannin tsaro bisa shawarar kiyaye tsaron duniya da ta gabatar, don neman tabbatar da tsaro ga kowa cikin hadin gwiwa.

ADVERTISEMENT

Yadda tsarin hadin gwiwar kasashen BRICS ke dada fadada, da yadda kasashen duniya ke gaggauta kaurace wa yin amfani da dalar Amurka, sai kuma yadda aka kafa cibiyar kula da harkokin shiga tsakani ta duniya, duk sun shaida sauyawar zamani da ma yadda kasashe masu tasowa suke ta kara fito da muryarsu ta neman adalci a duniya. Duk da yadda jiragen ruwan soja na Amurka ke zirga-zirga a tekun kudancin kasar Sin, yanayin da ake ciki na samun bunkasar kasa da kasa ta bai-daya ya tabbata. Bugu da kari, yadda wasu kasashe ke iya kokarin nuna fin karfi a duniya, ya shaida yadda suke dab da zuwa karshen yin haka. Duba da cewa, hadin gwiwar sassa daban daban shi ne jigon karnin da muke ciki a maimakon yaudara da fin karfi.

 

LABARAI MASU NASABA

Bikin Baje Koli CIIE, Bikin Zaburar Da Manoman Afirka

CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 

 

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bikin Baje Koli CIIE, Bikin Zaburar Da Manoman Afirka
Ra'ayi Riga

Bikin Baje Koli CIIE, Bikin Zaburar Da Manoman Afirka

November 12, 2025
CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 
Ra'ayi Riga

CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 

November 11, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari
Ra'ayi Riga

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutu Domin Bukukuwan Sallah

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutu Domin Bukukuwan Sallah

LABARAI MASU NASABA

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

November 16, 2025
Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

November 16, 2025
Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

November 16, 2025
Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

November 16, 2025
Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

November 16, 2025
DSS

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

November 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.