Jiya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron shugabannin kasashen BRICS karo na 14 ta kafar bidiyo, inda ya gabatar da muhimmin jawabi, tare da yin kira ga kasashen BRICS da su hada kai waje guda tare da samun karfin gwiwa.
Musamman, shirye-shiryen tsaro na kasa da kasa da ayyukan ci gaban duniya da shugaba Xi ya jaddada, sun dace da bukatun hadin gwiwar kasashen BRICS.
“Sanarwar Beijing” da aka amince da ita a wannan taron ta bayyana karara cewa, “Muna goyon bayan tattaunawar da ake yi tsakanin kasashen Rasha da Ukraine”, tare da aikewa duniya muryar kasashe masu tasowa na wanzar da zaman lafiya. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)