Bisa gayyatar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai isa birnin Kazan na Rasha, don halartar taron shugabannin kasashe mambobin BRICS karo na 16.
Tun daga shekarar 2013, shugaba Xi Jinping ya jagora, ko halarci duk tarukan shugabannin kasashe mambobin BRICS, tare kuma da gabatar da jawabai masu muhimmanci, kana ya fadada shawarwarin kasar Sin a muhimman fannoni, kamar ginawa, da bunkasuwa, da fadada tsarin hadin gwiwa na BRICS, da ba da gudummawar hikimar kasar Sin, da jagorantar hadin gwiwar BRICS don samun ci gaba mai dorewa.
Bana ita ce shekara ta farko ta “Hadin gwiwa bayan habakar BRICS”. Kasashen duniya suna sa ran yin taro na farko tsakanin shugabannin su, tun bayan da aka kara sabbin mambobi na “babban iyalin BRICS”, don shata tsarin ci gaban tsarin hadin gwiwa na BRICS, da samar da wani sabon zamani na hadin kai, da kara karfi ga kasashe masu tasowa, tare da habaka zaman lafiya da ci gaban duniya. (Safiyah Ma)