Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce hadin gwiwar raya tattalin arziki, cinikayya da makamashi tsakanin Sin da dukkanin kasashen duniya, ciki har da Rasha yana kan turba, bai sabawa doka ba, kuma ba abun zargi ba ne.
Lin Jian, ya bayyana hakan ne a Litinin din nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, bayan da aka jiyo Amurka na yiwa kasashe membobin kungiyar G7, da na kungiyar hadakar tsaro ta NATO, matsin lambar su kakabawa Sin karin harajin kwastam, saboda tana sayen mai daga Rasha.
Jami’in ya ce “Matakan Amurka cin zali ne daga bangare guda, kuma matsin lamba ne irin na tattalin arziki. Irin wadannan matakai na matukar yin karan-tsaye ga dokokin kasa da kasa na tattalin arziki da cinikayya, suna kuma barazana ga tsaro, da daidaiton tsarin sarrafawa da shigar da hajojin masana’antu sassan duniya. Kazalika, tun tuni an gamsu cewa matsin lamba ba zai samu karbuwa ba, kuma ba zai warware duk wasu matsaloli da ake fuskanta ba”.
Har ila yau, Lin ya ce matsayin kasar Sin dangane da rikicin kasar Ukraine bai sauya ba, cewa tattaunawa, da gudanar da shawarwari ne kadai hanyoyi mafiya dacewa na warware rikicin. Har kullum Sin na kan turbar adalci game da rikicin, tana kuma ci gaba da ingiza bukatar komawa teburin shawara tun barkewar rikicin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp