“Yanzu ba mu damuwa da ruwan sha da lantarki, muna godiya ga aminanmu Sinawa wadanda suka taimaka mana wajen gina tashoshin samar da wutar lantarki da kafa fitilu da haka rijiyoyi.” Shugaban kauyen Koniobla, malam Jean Doumbia ne ya fadi haka cikin farin ciki, lokacin da ya ga sabbin fitilu na haskaka titi da ma hasumiyar samar da ruwa da aka gina a kauyen.
Kasar Mali ta dade tana fama da matsalar karancin wutar lantarki, inda kauyukanta da suka samu damar yin amfani da lantarki bai kai kaso 20% ba. Kauyen Koniobla yana kudu maso gabashin birnin Bamako, kuma kusan ba a samun lantarki a kauyen, inda mazauna kauyen su kan shiga dogon layi don su debo ruwa daga wasu rijiyoyi da ke cikn kauyen. Amma hakan ya sauya bayan da kamfanin kasar Sin ya kammala shirin samar da wutar lantarki da zafin rana a wasu kauyuka biyu da suka hada da Koniobla da Karan na kasar ta Mali a bara, inda aka kafa tsarin samar da wuta da zafin rana da ma tsarin fitilun titi da tsarin samar da ruwan famfo da zafin rana da sauransu, wadanda suka amfani al’ummar wurin sama da su dubu 10.
- Me Ya Sa Dandalin FOCAC Ke Samun Karbuwa A Tsakanin Al’ummar Nahiyar Afrika?
- Xi: Sin Da Afirka Sun Zamo Sassa Na Farko Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya
Daga nan, ko da an shiga duhun dare, ana samun hasken fitilu a kauyukan, kuma ko yaushe ana iya samun ruwa mai tsabta da famfo da ke aiki da lantarki, har ma karin magidanta na kauyen suka sayi talabijin.
Kamar yadda Mali take, matsalar karancin makamashi na yi wa bunkasuwar akasarin sassan Afirka tarnaki. Duk da haka, Allah ya albarkaci Afirka da makamashi masu tsabta, irinsu makamashin iska da na rana, wanda hakan ya samar da dama ta warware matsalar. Abin da ya faru a kauyen Koniobla, ya shaida yadda Sin da kasashen Afirka suke hadin gwiwa da juna a wannan fanni tare da haifar da nasara.
A hakika, bisa tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da ma shawarar ziri daya da hanya daya, kasar Sin ta aiwatar da daruruwan shirye-shirye na samar da makamashi masu tsabta a kasashen Afirka. Misali a Nijeriya, tashar ruwa ta samar da wuta ta Zungeru da kamfanin kasar Sin ya gina ya kasance irinta mafi girma a kasar, wanda ke samar da lantarki da zai iya biyan bukatun birane masu girman Abuja guda biyu, sai kuma a bara, aka kaddamar da motocin safa masu aiki da lantarki na farko da kamfanin kasar Sin ya kera a birnin Lagos…
Kasancewar dukkansu kasashe masu tasowa, kasar Sin ta san tabbatar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba hanya ce daya tilo da za ta daidaita matsalar sauyin yanayi, da kuma tabbatar da dauwamammen ci gaba, haka kuma ta san yadda kasashen Afirka ke matukar fatan ganin samun bunkasuwarsu, da ma kalubalen da suke fuskanta, don haka take son raba nasarorin da ta cimma a fannin tabbatar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba.
Yanzu haka taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na gudana a birnin Beijing, kuma batun tabbatar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba na daya daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankalin mahalarta taron. Muna da imani kan cewa, Sin da kasashen Afirka za su tsara sabbin shirye-shiryen hadin gwiwa a wannan fanni, don tabbatar da dauwamammen ci gaba a kasashen Afirka.