Kasashen Afirka da dama ciki har da Najeriya sun dade suna fama da matsalar karancin wutar lantarki, sai dai wani rahoto na baya-bayan nan da kungiyar Ember mai nazarin makamashi ta duniya ta fitar, ya nuna cewa wannan yanayi yana canzawa.
Ta la’akari da yadda kasar Sin take samar da kaso 80% na allunan sola masu samar da wutar lantarki daga hasken rana na duniya, rahoton ya yi nazari a kan alkaluman shigar da allunan sola daga kasar Sin zuwa kasashen Afirka, tsakanin watan Yulin 2024 zuwa watan Yunin 2025, inda sakamako ya nuna cewa:
1. Yawan allunan sola da aka shigar da su Afirka ya karu da kaso 60%;
2. Karuwar shigar da allunan sola ta shafi kusan dukkan kasashen Afirka, inda jimillar wasu kasashe 20 a fannin ta kai matsayin koli a tarihi;
3. Karuwar allunan sola ta samar da damar samun karin wutar lantarki, inda ake sa ran samun karuwar wutar lantarki da za ta kai fiye da kaso 5% a wasu kasashe 16 dake nahiyar Afirka.
Tambaya ita ce: me ya sa allunan solan kasar Sin samun karbuwa a Afirka? Domin suna da araha, gami da inganci.
Kamar yadda muka sani, ana sayar da allon sola mai karfin watt 420 kan farashin kusan dalar Amurka 60 a Najeriya, kuma yana iya samar da wutar lantarki na kWh 550 a duk shekara. Sai dai idan za mu ci gaba da samar da wutar lantarki ta janareta mai amfani da man dizal, kamar yadda aka saba yi, to, a farashin man dizal na yanzu na dala 0.66 kan lita daya, man dizal na dala 60 zai samar da kWh 275 na wutar lantarki ne kawai. Wannan yana nufin cewa, ta hanyar amfani da allunan sola, kudin da aka yi tsiminsa zai biya kudin da aka kashe cikin watanni shida kacal. Ba a ma maganar saukin amfani, da damar biyan bukatar kare muhalli da allon ke da su.
Sa’an nan, na san tabbas ana mamakin yadda allunan sola, da suka yi tsada a baya, suka yi araha a yanzu. Wannan ya faru ne saboda manufar kasar Sin ta bunkasa makamashi mai tsafta, ta kawo sauye-sauye ga yanayin kasuwar makamashi ta duniya.
Tsakanin shekarar 2021 da ta 2025, kasar Sin ta gina tsarin amfani da makamashi da ake iya sabuntawa mafi girma da saurin ci gaba a duniya, wanda ya sa karfin kasar na samar da wutar lantarki ta makamashin da ake iya sabuntawa, ya karu daga kaso 40% zuwa kimanin kaso 60%. A sa’i daya kuma, kasar Sin ta zama kasa ta farko wajen fitar da fasahohin makamashi mai tsafta a duniya, wadda take fitar da na’urorin samar da wutar lanarki daga hasken rana da iska zuwa kasashe da yankuna sama da 200. Ci gaban fasaha na kasar Sin da kuma karfinta na samar da dimbin kayayyaki cikin sauri sun tabbatar da rahusar kayayyakinta, da ba su damar samun karbuwa a tsakanin al’ummun kasashe daban daban. Bisa wani bincike da shafin yanar gizo na Carbon Brief da ke Burtaniya ya yi, cikin shekaru goma da suka gabata, kasar Sin ta taimaka wajen rage matsakaicin kudin da ake kashewa domin samar da wutar lantarki daga hasken rana da kaso 80%.
Albarkacin cudanya da kasuwanci da ake yi tsakanin Sin da Afirka, sannu a hankali sararin samaniyar Afirka na kara haskakawa da dare. Amma wannan mafari ne kawai. Saboda a bangare guda, nahiyar Afirka ce ke da kaso 40% na zafin hasken rana a duniya, da kaso 32% na karfin iska, da kaso 12% na karfin ruwa. A daya hannun kuma, neman ci gaban tattalin arziki da kare muhalli a lokaci guda, wani muhimmin jigo ne a hadin gwiwar Sin da Afirka. A cikin ‘yan shekarun nan, kasar Sin ta aiwatar da daruruwan ayyuka masu alaka da makamashi mai tsafta, da aikin raya tattalin arziki ta hanyar kare muhalli a Afirka. Ta hanyar musayar fasahohi, da hadin gwiwa kan wasu ayyuka, da samar da tallafi a bangaren hada-hadar kudi, kasar Sin na kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin ta da kasashen Afirka a fannin raya makamashi mai tsafta. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp