An gudanar da bikin cika shekaru 30 da kafuwar asusun hadin gwiwar kasashe masu tasowa na MDD a birnin New York, babban birnin Amurka.
Yayin bikin, zaunannen wakilin Sin dake MDD, Fu Cong, ya fitar da jawabi cewa, bangaren Sin ya yaba da sakamakon hadin gwiwa mai inganci da asusun ke goyon baya. Kuma Sin za ta ci gaba tsayawa tsayin daka kan goyon bayan ginshikin ci gaban MDD, da goyon bayan ra’ayin bangarori daban daban na gaskiya da kuma daukar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashe masu tasowa a matsayin abin dake kan gaba a cikin hadin gwiwar da Sin ke yi da kasashen waje.
An kafa asusun hadin gwiwar kasashe masu tasowa a shekarar 1995, wanda ofishin kula da hadin gwiwar kasashe masu tasowa na MDD ke gudanarwa, da nufin habaka ci gaba mai dorewa da kawo sauyin fasaha ta hanyar hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da kuma taimaka wa kasashen su iya magance kalubalen ci gaba tare.(Safiyah Ma)