• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin Gwiwar Sin Da Turai Zai Yaukaka Daidaiton Dangantaka

by CGTN Hausa
1 year ago
Turai

Ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke gudanarwa a kasashen Faransa, da Serbia, da Hungary, ta kasance muhimmin matakin yaukaka dangantakar diflomasiyyar bangarorin biyu.

Kasar Sin da kasashen Turai karkashin jagorancin kungiyar EU, muhimman bangarori ne biyu dake ingiza manufar samar da tasirin fada-a-ji daga bangarori daban daban, kuma sassan biyu na matukar goyon bayan dunkulewar duniya, a bangare daya kuma, sun kasance bangarori masu rungumar mabanbantan wayewar kai a duniya. Don hake ne ma masharhanta da dama ke kallon alakar Sin da Turai a matsayin mai da matukar muhimmanci wajen saita akalar ci gaban duniya baki daya.

  • An Gabatar Da Shirin Talabijin Mai Suna Labarun Da Xi Jinping Ya Fi So A Hungary
  • Shugaba Xi: Har Kullum Sin Da Hungary Na Kallon Alakarsu Daga Mahanga Mai Fadi Da Wa’adi Mai Tsawo

Masu fashin baki na ganin cewa, Sin da kasashen tarayyar Turai ba su da manyan banbance-banbancen neman cimma moriya, ko sabani ta fuskar siyasar yankunan su. Kaza lika, batutuwan da suke dunkule sassan biyu wuri guda, sun rinjayi banbance-banbancensu. Hakan ne kuma ya sa har kullum suke ta kokarin yaukaka alakar su, ta yadda za su ci gaba da kasancewa sahihan kawaye abun koyi, su kuma ci gaba da yin hadin gwiwa, da cimma moriya tare a yanzu da ma nan gaba.

A bangarenta, a ko da yaushe kasar Sin na daukar tarayyar Turai a matsayin muhimmin karfi dake da tasiri a harkokin kasa da kasa, tana kuma sanya batun raya dangantakarta da EU a sahun gaba cikin harkokin diflomasiyyarta.

Bisa hakan ne ma a bazarar shekarar 2014, shugaba Xi ya ziyarci helkwatar kungiyar EU, inda a lokacin ya gabatar da shawarar hada karfi da karfe tsakanin kasarsa da EU, a fannonin wanzar da zaman lafiya, da samar da ci gaba, da gudanar da sauye-sauye, da bunkasa wayewar kai. Har yanzu kuma wannan kuduri bai sauya ba, yana kuma ci gaba da zama alkiblar raya dangantakar sassan biyu a halin da ake ciki yanzu.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

Yayin da duniya ke kara tsunduma cikin hali na rashin tabbas, da rigingimu nan da can, yana da kyau Sin da EU su wanzar da tattaunawa ta kut da kut, su kuma mayar da hankali ga hadin gwiwar cimma moriyar juna, daga fannin ingiza ci gaban bangarorin biyu zuwa tunkarar kalubalolin dake addabar duniya baki daya.

Tabbatattun shaidu sun nuna cewa, muddin Sin da EU sun yi aiki tare wajen saita alkiblar da za su bi domin bunkasa kan su, ko shakka babu hakan zai iya kai su ga cimma burikan da suka sanya gaba, tare da haifarwa alummun su da tarin alherai.

A halin da ake ciki, Sin na kan gaba a jerin sassa mafiya muhimmanci ga Turai a fannin hada-hadar cinikayya. Duk da tafiyar hawainiya da tattalin arzikin duniya ke yi a yanzu, a shekarar bara, jimillar darajar cinikayya tsakanin Sin da EU ta kai dala biliyan 783. Kaza lika Sin na yiwa Turai maraba a fannonin cin gajiyar hadin gwiwar kasuwanci, da raya kimiyya da fasaha, da bunkasa hidimomin sarrafa hajojin masanaantu da rarraba su ga sassan duniya, ta yadda sassan biyu za su ci gajiyar bai daya, da samun nasara da walwala tare.

Ko shakka babu sannu a hankali, hadin gwiwar Sin da Turai na bunkasa, musamman ma a fannonin da duniya ke mayar da hankali yanzu a kansu, kamar tattalin arziki na dijital, da bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da cin gajiya daga sabbin makamashi, da kirkirarriyar basira.

Bunkasar Sin wata dama ce ga EU, kana daidaita kawancen sassan biyu zai taimaka matuka wajen shawo kan kalubale da EU ke fuskanta. A halin da ake ciki, karin sassan Turai na dada fahimtar muhimmancin hada gwiwa da Sin, wajen magance matsalolin makamashi, da hauhawar farashin hajoji da EU ke fuskanta, a daya bangaren dangantakar sassan biyu za ta kyautata takara mai tsafta tsakaninsu, da haifar da gajiya ga Sin da turai da ma duniya baki daya. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin
Daga Birnin Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a
Daga Birnin Sin

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

October 29, 2025
Next Post
Lokaci Ya Yi Da Za A Kara Dakon Zumunci A Tsakanin Sin Da Serbia

Lokaci Ya Yi Da Za A Kara Dakon Zumunci A Tsakanin Sin Da Serbia

LABARAI MASU NASABA

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

October 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

October 29, 2025
COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

October 29, 2025
Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

October 29, 2025
Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci

Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci

October 29, 2025
Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.