• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin Gwiwar Sin Da Yankin Turai Na Kara Kawo Haske Ga Tattalin Arzikin Duniya

by Sulaiman
5 months ago
Sin

Duk da za a iya cewa husumar cinikayya da Amurka ta tayar a duniya ta fara kwanciya musamman saboda tattaunawa da shawarwari da ake yi, tabbas halin rashin tabbas da tattalin arzikin duniya yake fuskanta a shekarar 2025 ya tsananta da yawa. Sai dai kuma, idan an duba wasu sassa na daban, za a iya ganin bullar hasken rana, saboda dama ba zai yiwu a dauwama a cikin duhu ba. 

Daya daga cikin bangarorin da za su bayar da kwarin gwiwa kan halin da ake ciki shi ne hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da yankin Turai. A shekarar nan ta 2025 ake cika shekaru 50 da kulla alakar diflomasiyya a tsakanin Sin da Turai. Cikin wadannan shekarun, harkokin cinikayya da tattalin arziki na ci gaba da samun habaka.

  • An Kama Sojoji 18 Da ‘Yansanda 15 Da Suke Siyar Da Makamai Ga ‘Yan Ta’adda
  • Masu Bincike Na Sin Sun Cimma Sabon Sakamako A Fannin Saurin Sadarwa Tsakanin Tauraron Dan Adam Da Doron Duniya

Zuwa karshen shekarar 2024, kamfanonin yankin Turai sun zuba jarin da ya kai zunzurutun kudi fiye da dala biliyan 150 a kasar Sin, yayin da ita ma Sin ta zuba jarin kusan dala biliyan 110 a yankin, kamar yadda aka ruwaito daga mataimakin ministan harkokin cinikayya na kasar Sin Yan Dong.

Wannan hadin gwiwa ba ga sassan biyu kawai yake da matukar muhimmanci ba, har ma ga duniya, kasancewar Sin ita ce ta biyu a karfin tattalin arziki a duniya, inda yankin Turai kuma yake matsayin na uku. Don haka hadin gwiwarsu yana da muhimmiyar rawar takawa game da sha’anin tattalin arzikin duniya saboda idan aka hade hada-hadar cinikayyarsu wuri guda, su ne suke da kashi daya bisa ukun jimillar cinikayyar duniya.

Kamfanonin bayar da hidimomi kamar irin su MBB Logistics mai ba da hidima ga Amazon, da katafaren kamfanin cinikayya ta shafin intanet mafi girma na Poland sun samu karin kuzarin kasuwanci sakamakon fadada layin dogo da ya sada Sin da yankin tsakiyar Asiya zuwa Turai, inda ya kara yawan manyan cibiyoyinsa na tara kayayyaki. MBB logistics yana samar da hidimomi da sufuri na ketare ga kayayyakin da dandalolin kasuwanci ta intanet na kasar Sin guda 300 suke hada-hadarsu. Wannan na taimakawa wajen habaka kasuwanci tsakanin Sin da Turai.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Kazalika, tashar teku ta Duisburg dake kasar Jamus ta kasance cibiyar sufurin layin dogo a tsakanin Sin da yammacin Turai, inda yawan kwantenonin da ake hada-hadarsu a tashar duk shekara suka kai miliyan hudu. Bugu da kari, sufurin layin dogo da ya sada Sin da Turai ya kara bude hanyoyin zuba jarin kamfanonin Sinawa a Duisburg. Sannan ana ci gaba da inganta sufurin dogo ta hanyar sabbin tsare-tsaren da ake kawowa kamar su na jirgin Tea Train da na dakon motocin sabbin makamashi da ake fitarwa zuwa waje, watau New Energy Vehicle Export Train, domin raya cinikayyar Sin da Turai.

Har ila yau, layin dogo na Budapest zuwa Belgrade da ya sada kasashen Serbia da Hungary mai kusan tsawon kilomita 350 a karkashin kawancen BRI wani sabon yunkuri ne na cimma muradun kasar Sin da yankin Turai a kan amfani da makamashi mai tsafta a karkashin kawancen na BRI.

Akwai kuma karin kamfanonin Sin dake aikin inganta amfani da makamashi mai tsafta a tashar tekun Piraeus ta kasar Girka, kana a yankin kudu maso gabashin kasar Malta, kauyen kamun kifi na Marsaxlokk da ya sha fama da matsalar gurbacewar yanayi sakamakon gina tashar lantarki tun a farko-farkon shekarun 1990, a halin yanzu ya samu waraka tun bayan da wani kamfanin Sin ya gyara tashar tare da jan ragamar tafiyar da ita, inda aka samu raguwar hayaki mai gurbata muhalli da ake fitarwa. Duka wadannan misalai, suna nuna yadda kawancen Sin da yankin Turai ke kara armashi da kuma kawo haske ga tattalin arziki. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani
Daga Birnin Sin

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Next Post
Miƙa Mulki Daga Buhari Zuwa Tinubu: Abubuwan Da Suka Fi Jan Hankali

Tinubu Ya Yi Ƙoƙari, Gyaran Nijeriya Aikin Kowa Da Kowa Ne – Buhari

LABARAI MASU NASABA

Sin

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

October 27, 2025
Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

October 27, 2025
Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

October 27, 2025
Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

October 27, 2025
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

October 27, 2025
Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.