• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

“Hadin Kan Kasashen BRICS” Ya Karfafa Shawo Kan Kalubale

by CGTN Hausa and Sulaiman
1 month ago
BRICS

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

A halin yanzu, sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin karni guda suna ci gaba da habaka cikin sauri, yayin da mulkin kama-karya, son kai, da kuma kariyar tattalin arziki suka kara yawaita. A wannan yanayi, a wajen taron yanar gizo na shugabannin kasashen BRICS da aka gudanar a ran 8 ga watan nan da muka ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da shawarwari uku don karfafa “hadin kan kasashen BRICS” da kuma kafa kyakkyawar makomar bil’adama ta bai daya. Wato na farko nacewa ga kasancewar mabambantan bangarori a duniya. Bugu da kari, a kare adalcin duniya domin ci gaba da bude kasuwanci don samun nasara ga kowa, da kuma kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya. Sannan a karfafa hadin kai don habaka ci gaban juna.

Wadannan shawarwari uku ba kawai sun nuna sabbin ayyuka da aikin da ke gaban kasashen BRICS ba, har ma sun ba da hanyoyin habaka ingancin hadin kan BRICS, ta yadda za ta zama karfi na farko a cikin sauye-sauyen tsarin daidaita harkokin duniya. A matsayin babbar kungiyar kasashe masu tasowa, tsarin hadin gwiwar BRICS tun daga shekarar 2006 ya ba da fa’ida ga kasashe masu tasowa, kuma ya zama karfi mai kwazo, daidaito, da kyautatawa a harkokin duniya.

Kasancewar mabambantan bangarori a duniya shi ne tushen zaman lafiya da ci gaba. Game da wasu kasashe dake amfani da kasuwanci a matsayin makamin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wasu, Sin ta ba da shawarar ci gaba da bude kofa da cin moriya tare da kuma kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya. Wannan ya sami amincewar shugabannin da suka halarci taron, kuma ya ba da karin tabbaci ga al’ummar duniya. Daga taron tattaunawa kan zuba jari na kasa da kasa na Sin (CIFIT) da taron hada-hadar ba da hidima (CIFTIS), har zuwa bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga ketare (CIIE) da za a gudanar a watan Nuwamba, Sin ta dauki hakikanin matakai don raba damammaki da samun nasara ta hanyar bude kofarta ga kasashen BRICS, da kuma inganta tattalin arzikin duniya mai bude kofa, don bai wa kasashe masu tasowa karin damammaki shiga cikin hadin gwiwar duniya da raba sakamakon ci gaba yadda ya kamata.

Dabara ta rage ga mai shiga rijiya, dole ne a inganta harkokin cikin gida ta yadda za a iya shawo kan kalubalen waje da kyau. A nan gaba, hadin gwiwar BRICS zai samar da karin sakamako a fannonin kasuwanci, kudi, da fasaha, don kara karfafa tushen “hadin kan kasashen BRICS,” da kara karfi da tasirinsa baki daya. (Amina Xu)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa
Daga Birnin Sin

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Next Post
Xi Jinping Ya Aika Da Sakon Taya Murnar Bude Taron CIFTIS Na Shekarar 2025

Xi Jinping Ya Aika Da Sakon Taya Murnar Bude Taron CIFTIS Na Shekarar 2025

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

October 25, 2025
Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Thomas Etuh: Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025

October 25, 2025
Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025
Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.