• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin ‘Yam Balls’ Mai Kayatarwa

by Bilkisu Tijjani
2 years ago
Yam Balls

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ake Gurasa Ta Semovita

Yadda Ake Lemon Tsamiya (Tamarin Juice)

Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake saduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu na Girki Adon Mata.

Wannan makon za mu yi magana ce akan hadaddan yam bolls, wanda gaskiya Uwargida yana da kyau ga dadi sai kin gwada za ki gane.

  • Real Madrid Na Zawarcin Harry Kane Domin Maye Gurbin Benzema
  • Sojoji Sun Yi Nasarar Kashe ‘Yan Ta’adda 6 Da Kwato Makamai Da Dama A Kaduna

Abubuwan da ya kamata Uwargida ki tanada:

Doya, Kwanfilaiks, Fulawa, Kwai, Nama, Mai, Albasa, Tattasai ko Attaruhu, Magi, Gishiri, Kuri, ko kayan kamshi duk abin da kike da shi na kamshi:

Da farko za ki dafa doya ta dahu so sai ta yi luguf sai ki ajiye ta a gefe sannan ki dafa naman ki shima ya dahu so sai yadda zai daku ko kuma cakudawa.

Idan kika daka naman ko kika cakuda shi, sannan ki dakko abin suyarki ki dora shi a wuta ki zuba masa mai kadan haka sannan ki zuba albasa wadda dama kin yayyanka ta ko kin daka ta ya danganta da yadda kike son ta sai ki kawo tattasanki ko attaruhun duk wanda kike so wanda dama kin jajjaga su sai ki zuba su ki dan soya su sama-sama.

Sannan sai ki dakko naman da kika yi miding din shi ki zuba kina juyawa amma ki rage wuta sannan ki kawo magi, gishiri da kayan kamshi ki zuba kina juyawa idan ya dan soyu sai ki sauke shi sannan ki sake daka tattasan da albasa sai ki dora abin suya ki sa dan mai ki zuba albasar da tattasan ki dan soya su sama-sama haka, sannan ki kawo kayan kamshi ki zuba tare da onga na miyar ja sai ki sa magi, gishiri ki dan kara soyawa sannan ki sauke shi sai ki faffasa doyar ko ki daka ta ta yi laushi sosai kamar ta sakwara sannan ki kawo tattasan da kika soya ki zuba sai ki gauraya su ya mulke tare da doyar tun da dama mun ce ta yi laushi kamar ta sakwara, sannan ki dakko wannana naman da kika soya sai ki ciccura shi ya yi bolls.

Idan kika gama sai ki koma kan doya kina dibanta kamar yadda za ki cura ta sai ki dan bubbuda ta ta yi fadi sai ki dakko wannan naman da kika yi bolls dinsa guda daya ki sa a ciki sai ki rufe shi ki yi boll da shi kin ga naman yana ciki tsakiya kenan doyar ta rufe naman.

Haka za ki yi ta yi har ki gama, sannan kina sa su a fulawa ki fitar ki sa a ruwan kwai ki fitar, sannan ki sa a kwamfilanks wanda dama kin dan daka shi sai ki dan mammatsa shi saboda kwamfilanks din ya shisshiga ciki sannan ki dora abin suya a wuta ki zuba masa mai, mai dan yawa daman abin suyar mai zurfi za ki samu sai ki bar man ya yi zafi so sai sannan ki fara zubawa kina soyawa haka za ki yi ta yi har ki gama.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Ake Gurasa Ta Semovita
Girke-Girke

Yadda Ake Gurasa Ta Semovita

October 12, 2025
Yadda Ake Lemon Tsamiya (Tamarin Juice)
Girke-Girke

Yadda Ake Lemon Tsamiya (Tamarin Juice)

October 4, 2025
Yadda Ake Hada Sushi
Girke-Girke

Yadda Ake Hada Sushi

September 27, 2025
Next Post
An Kaddamar Da Makon Fim Na Ziri Daya Da Hanya Daya A Shanghai

An Kaddamar Da Makon Fim Na Ziri Daya Da Hanya Daya A Shanghai

LABARAI MASU NASABA

Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.