Jiya na karanta wani bayanin da ya burge ni da wani dan jarida na kasar Najeriya mai suna Olatunji Saliu ya rubuta. Dan jaridan ya shiga jirgin kasa daga birnin Lagos zuwa Ibadan, a lokacin hutun sabuwar shekara, inda ya shaida yadda layin dogon da kamfanin kasar Sin ya gina ya taimakawa jama’ar Najeriya wajen haduwa da iyalansu. Matafiya dake cikin jirgin na cikin farin ciki da annashuwa, yayin da suka tuna da wahalar zirga-zirga da aka fuskanta a baya, sun kuma yaba da irin matakan tsaron da ke cikin jirgin kasa baya ga sauri, da walwala, gami da araharsa. Sun ce samun jirgin kasan, ya sa marasa karfi suna iya haduwa da iyalai da ke wurare masu nisa, matakin da ya kawo karshen matsalar shiga mota. Ban da wannan kuma, an samu damammakin raya ciniki da aikin yawon shakatawa. A zahiri, wannan layin dogon ya samar da alfanu ga jama’a. Ma iya cewa, Kwalliya ta biya kudin sabulu.
Sai dai a wani lokaci, a kan shiga yanayi mai sarkakiya, yayin da ake kokarin gina layin dogo. A kwanan nan, kafofin watsa labaru na kasashen yamma suna ta kokarin ruruta wani shiri mai taken “the Lobito Corridor”, da kasar Amurka, da kungiyar hadin kan kasashen Turai ta EU, gami da sauran wasu bangarori ke shirin gudanarwa. Wannan aiki ya shafi gina wasu layukan dogo guda 2, wadanda tsawonsu ya kai fiye da kilomita 100, don hada wasu tsoffin layukan dogo na kasashen Kongo Kinshasa, da Zambia, da Angola, ta yadda za a fito da ma’adinai na kasashen zuwa kasashen yamma, inda za a bi ta tashar jirgin ruwa ta Lobito ta kasar Angola. Wannan aiki dai ba shi da wani sarkakiya, sai dai kafofin watsa labaru na kasashen yamma sun kambama shi a matsayin “martanin da gwamnatin kasar Amurka ta mayar kan shawarar ‘Ziri Daya da Hanya Daya’ ta kasar Sin”. Har ma gidan rediyon muryar Amurka VOA, ya yi amfani da taken wai “ Kasar Amurka ta zuba jari a nahiyar Afrika don takara da kasar Sin”, da “ Kasar Amurka za ta maye gurbin kasar Sin a fannin gina kayayyakin more rayuwa a nahiyar Afrika”, yayin da yake gabatar da rahotanni dangane da batun.
- Ma’aikatar Kasuwanci: Kasar Sin Tana Da Kyawawan Sharuddan Jawo Jarin Waje
- Xi Ya Jaddada Bukatar Samun Cikakkiyar Nasara Wajen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa
Sai dai a ganina, akwai abubuwa marasa dacewa a cikin ra’ayin kasashen yamma. Tun da yake ana son zuba jari a nahiyar Afrika, ya kamata a mai da hankali kan taimakawa kasashen Afirka don su samu ci gaba ko? Amma maimakon haka, sai ake tabo maganar takara da kasar Sin. To, me ya kawo batun takara?
Hakika game da shirin hadin gwiwa na gina ababen more rayuwa, da sauran kasashe suka gabatar, kasar Sin har kullum ta kan nuna goyon baya a kai. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sha jaddadawa cewa, akwai isassun damammaki na hadin gwiwa a fannin gina kayayyakin more rayuwa a kasashe daban daban, don haka bai kamata a ce takara ta zama wata matsala, ko wani ya maye gurbin wani, tsakanin mabambantan shirye-shiryen da aka gabatar ba. Kasar Sin tana goyon bayan duk wani shiri da zai taimaka wajen kulla huldar hadin kai, da inganta kayayyakin more rayuwa a duniya. Sai dai yunkurin takara a bangaren siyasa, ta hanyar fakewa da batun raya kayayyakin more rayuwa, ba zai taba cin nasara ba, in ji ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin.
Hakika, a matsayinta na sahihiyar abokiyar kasashen Afrika, kasar Sin ta yi hadin kai tare da kasashen Afrika, wajen gina layin dogo na fiye da kilomita dubu 10, da hanyoyin mota da suka kai kimanin tsawon kilomita dubu 100, da gadoji kimanin dubu 1, gami da tashoshin jiragen ruwa fiye da 100, duk a kasashen Afrika, cikin shekaru 20 da suka gabata. Ganin haka zai sa a fahimci muhimmancin kasar Sin, da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da ta gabatar, a fannin raya bangaren kayayyakin more rayuwa a nahiyar Afrika. Wai ana iya maye gurbinsu da wani aikin gini daya kadai wanda bai ma fara aiki ba tukuna?
Watakila su mutanen kasashen yamma sun fi dora muhimmanci kan takara, da shawo kan wani, sakamakon al’adu da tarihin su. Amma a ganin Sinawa, abu mafi muhimmanci shi ne tabbatar da daidaito, da hadin kai, da amfana da juna, gami da haifar da ci gaba, saboda ta wannan hanya ita kadai ake iya daidaita yanayin da duniyarmu ke ciki na rashin daidaito a fannin ci gaba. Nahiyar Afrika dake fama da raunin tattalin arziki, ba za ta iya samar da dimbin gudunmowa ga tattalin arzikin duniya ba. Don haka ya dace a ba kasashen Afrika damar raya kansu, daga baya za a samu damar raya duniyarmu yadda ake bukata. Wannan ra’ayi na daga cikin tunanin Sinawa na “Al’ummar dan Adam mai makomar bai daya”.
Maimakon a dora muhimmanci kan wane ne ya samu damar gina layin dogo a kasashen Afrika, ya kamata a tabbatar da cewa, za a samar da ci gaban tattalin arziki, da baiwa jama’a damar jin dadin rayuwa. Ina tsammanin Olatunji Saliu da sauran fasinjojin da ya gamu da su a cikin jirgin kasan, za su yarda da wannan ra’ayi. (Bello Wang)