Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) Malam Jalal Arabi ya yi kira ga tawagar ‘yan jarida da za su yi aikin bayar da rahottanin aikin hajjin bana daga kasa mai tsarki da su tabbatar da sun yi riko da gaskiya yayin da suke bayar da rahottaninsu.
Malam Arabi ya yi wannan kira ne a yayin da yake kaddamar da tawagar ‘yan jaridar a babban dakin taron hukumar da ke Abuja ranar Alhamis 9 ga watan Mayu 2024.
- Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso 5.7 A Watanni Hudu Na Farkon Bana
- Hadin Gwiwar Sin Da Turai Zai Yaukaka Daidaiton Dangantaka
Ya nemi ‘yan jaridar su guji yada jita–jita da labaran da za su bata suna da mutuncin Nijeriya a idon duniya.
“Na tabbatar da dukkan ku kwararru ne a fagen aikinku, amma ina tunatar da ku ne a kan bukatar mu na fatan a gudanar da aikin hajjin bana ba tare da wani rudani ba.
Tun da farko, Kwamishina a Hukumar mai kula da Tsare-tsare da Bincike, Farfesa Abubakar Yagawal, ya nemi ‘yan jarida su sa kishin kasa a gaban su a yayin da suke gudanar da aikinsu a kasa mai tsarki, ya kuma nemi su yi koyi da hadisin Manzon Allah (SAW), inda ya hori al’umma su fadi alhairi ko su yi shiru.
A martaninsa, shugaban tawagar ‘yan jaridar, wanda kuma shi ne mataimakin daraktan yada labarai na NAHCON, ya ce, “ Za mu yi aiki tare da kishin alhazai da kasa a gaba”.