Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Edo, Sheik Ibrahim Oyarekhua, ya bayyana cewa maniyyata 238 daga cikin 400 da za su yi aikin Hajjin bana a Jihar Edo ba za su samu Damar zuwa gudanar da ibadar ba a Kasar Saudiyya.
Sheik Ibrahim ya kuma bayyana cewa a ranar Asabar 2 ga watan Yuli ne za a yi jigilar maniyyata 162 a jihar zuwa kasa mai tsarki.
Malamin ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata a wata hira da ya yi da kamfanin jaridar Daily trust a Benin, Jihar Edo.
“Muna da mahajjata 400 da suka yi niyya, amma saboda jinkiri da cutar COVID-19 ta kawo a baya-bayan nan a 2020, 2021 da 2022, 162 ne kawai za a iya kwashe wa.
“Don haka, ma’aunin da muka yi amfani dashi wajen zabo maniyyatan shine, wadanda suka fara biyan kudin tafiyar sune gaba. Mun fara diba daga 2020, 2021 sannan 2022.”
Ya ce sun gama shirya dukkan tsare-tsare ta fuskar masaukin otal da abinci da sauran su.