Hukumar Jin dadin alhazai ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wata mahajjaciya mai suna Hadiza Isma’il, yar asalin karamar hukumar Madobi a kasar Saudiyya.
Hadiza Isma’il, ta rasu a ranar Litinin da misalin karfe 3:15 na rana agogon Saudiyya, bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya kamar yadda sanarwar shugaban tawagar manema labarai na Hajjin bana fitar, Sanusi Bature Dawakin-Tofa.
- Abba Gida-Gida Ya Bai Wa Alhazan Kano 6,166 Kyautar Miliyan 65
- Hajjin 2023: Maniyyata 156 Ba Za Su Samu Tashi Daga Jihar Kano Ba
Sanarwar ta ce, an kai matar mai shekaru 58 a asibitin NAHCON domin jinyar zazzabi kafin a kai ta asibitin Sarki Abdulaziz da ke Makkah inda aka tabbatar da rasuwarta.
Tuni dai aka binne ta a garin Makkah bayan yi mata sallar jana’iza a masallacin Haramin Makkah.
Babban Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai na Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu Danbappa ya mika sakon ta’aziyyarsa a madadin hukumar da Gwamnati ga iyalan mai rasuwar, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikanta da rahama, ya kuma baiwa iyalai hakurin rashinta.