Hukumar Alhazai ta Nijeriya, NAHCON ta kammala aikin tantance kamfanonin jiragen sama da na dakon kaya da za su rika jigilar maniyyatan Nijeriya da jakunkunansu zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin 2025.
An dauki tsauraran matakan tantancewa wanda aka shafe tsawon mako ana aiki, wanda aka fara a ranar 27 ga watan Nuwamba, kuma aka kammala ranar 5 ga Disamba, 2024, a hedikwatar NAHCON da ke Abuja.
- Sin: Daga 2018 An Gurfanar Da Mutane 114,000 Kan Laifuka Masu Nasaba Da Amfani Da Mukami Ba Bisa Ka’ida Ba
- “Akwai Bukatar Gwamnatocin Nijeriya Su Inganta Aikin Harkar Ma’adanai”
Kwamitin mambobi 32 ne suka gudanar da aikin tantancewar wanda Shugaban Hukumar Alhazai ta Nijeriya, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya kaddamar a ranar 26 ga Nuwamba, 2024.
Aikin tantancewar an yi shi ne don zabar amintattun kamfanonin jiragen sama da kamfanonin dakon kaya waɗanda suka cika ka’idojin aminci da ƙa’idoji na ƙasa da ƙasa. Wannan tsari yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da aikin Hajji mai aminci ga alhazan Nijeriya.
Ga jerin kamfanonin da aka tantance:
1. Max Air Limited
3. Flynas (Kamfanin Saudiyya),
4. Air Peace Limited,
5. Flyadeal (Kamfanin Saudiyya),
6. Gyro Air Limited,
7.Trebet Aviation,
8. Umrah Air Limited (Ethiopian Airline),
9. Value Jet,
10.Umza Aviation Services Limited.
11.Aglow Aviation Support Services Limited.
12. Kiswah Logistics Services Limited.
13.Sokodeke,
14.CargoZeal Technologies.
Bayan tantancewa, Za a sanar da jerin sunayen manyan jiragen da suka yi nasara. Bayan haka, za a sanya hannu kan amincewar yarjejeniyar kwangilar dakon maniyyata da kayayyakinsu don kammala ayyukan Hajji na 2025 a kan lokaci.