• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hajjin 2024: Abubuwan Da Suka Kamata A Sani

byBello Hamza
1 year ago
Hajjin

Hukumar kididdiga ta kasar Saudiyya GASTAT ta fitar da cikakkun alkaluman da suka shafi aikin hajjin shekarar 2024, inda ta bayyana cewa alhazai 1,833,164 ne suka gudanar da aikin hajjin bana a Makka. Wanda hakan ya nuna yadda Alhazai dabam-dabam daga sassan duniya suka halarci aikin Hajjin Bana.

A bangaren jinsi a tsakanin Alhazan wannan shekarar, an samu maza 958,137 da mata 875,027 a gaba ki dayan Alhaza da suka gabatar da ibadar. Mafiya yawa daga cikin mahajjatan da adadin da sun ya kai 1,611,310, sun fito ne daga kasashen ketare, yayin da 221,854 suka kasance mahajjatan cikin gida ‘yan kasar Saudiyya.

  • Kamfanin Kera Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Sin Ya Shiga Kasuwar Kenya
  • Mutane 75,000 Sun Kamu Da HIV, 45,000 Sun Rasu A Shekarar 2023 – NACA DG

Kason Nahiyoyin Da Suka Halarci Kasar Saudiyya

Kididdigar alkalumman yawan mahajjatan bana ta nuna kashi 63.3% na mahajjatan Asiyawa ne (wadanda suka fito daga yankin Asiya) wadanda ba Larabawa ba, wanda ya sa wannan ya zama rukuni mafi yawa a mahajjatan bana. Alhazan da suka kasance larabawa kuwa sun kunshi kashi 22.3%, sai kuma ‘yan Nahiyar Afirka wadanda ba larabawa da suka kunshi kashi 11.3%.

Sauran kashin kuma wadanda suka fito daga nahiyar Turai da Austrilia sun kunshi kashi 3.2% daga cikin yawan mahajjatan banan.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Hanyoyin Sufurin Da Akayi Amfani Da Su

Dangane da hanyoyin sufurin da aka yi amfani da su kuwa, mafi yawan alhazai wanda addadinsu ya kai 1,546,345, sun isa kasar ne ta jirgin sama. Sai kuma mahajjata kimanin 60,251 da suka shiga kasar Saudiyya ta Motaci da kuma jiragen kasa. Sai Kuma mahajjata 4,714 da suka isa kasar ta ruwa.

Rayukan Da Aka Rasa

Sai dai kash, a lokacin aikin Hajjin na bana, an yi asarar rayuka da dama. Ministan lafiya na Saudiyya ya tabbatar da cewa mahajjata 1,301 ne suka rasu a yayin gudanar da aikin hajjin. Musamman ma, kashi 83% na wannan mace-macen sun shafi mutanen da ba su da ingantacciyar takardar izinin gudanar da aikin Hajjin ne.

Alkaluma da abubuwan da suka faru na Hajjin 2024 sun nuna yadda ibadar aikin hajjin ke tara mutane daga sassa daban-dabam na duniya da kuma irin yadda al’ummar muslulmi a duniya suka dauki ibadar da ta kasance cikin rukunai ko ginshikai na addinin musulunci.

Duk da irin kalubalen da ake fuskanta, miliyoyin musulmi sun yi nasarar kammala wannan aikin na ibada, lamarin da ke nuni da jajircewa da sadaukarwar mahajjata da kuma irin kokarin da mahukuntan Saudiyya suke yi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Rarara

'Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Rarara

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version