Domin kyautata gudanar da aikin hajji da kuma saukaka wa maniyyata, Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON), za ta sabunta ka’idojin ciyar da alhazai da masaukansu a kasa mai tsarki.
Mukaddashin Shugaban NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya shaida hakan a ranar Talata, yayin da yake kaddamar da kwamitin da za su sake duba ka’idojin masaukan alhazan da masu aikin dafa musu abinci.
Arabi ya kara da cewa, sake nazartar ka’idojin da ake bi a kan ciyar da alhazan da masaukansu, zai taimaka sosai wajen inganta aikin hidimta wa Alhazan Nijeriya tare da kyautata jin dadi da walwalarsu.
- Gwamnatin Kaduna Ta Kaddamar Da Kwamitin Mutum 8 Don Inganta Harkokin Aikin Hajjin 2024
- Kamata Ya Yi Kasashe Masu Ci Gaba Sun Cika Alkawarin Da Suka Yi Na Samar Da Kudaden Taimakawa Kasashe Masu Tasowa Wajen Tinkarar Sauyin Yanayi
A karshe, ya mika wa kwamitin kundin tsarin dokar da zimmar duba hanyoyin da suka dace, domin yin garanbawul ga wuraren da ake da bukatar yin gyara, saboda kwalliya ta biya kudin sabulu na kyautata walwala da jin dadin alhazan yayin da suke can Kasar Saudiyya.
A cewarsa, akwai bukatar yin garanbawul ga tsarin ayyukan a hidimar aikin hajji, domin tafiya daidai da tsarin zamani wadda duniya ke kai a halin yanzu.
“Abun da muke yi yanzu shi ne, duba hanyoyin da suka dace domin inganta al’amura, kamar yadda take gudana a wasu sassan duniya, sannan muna bukatar kwarin guiwa da kuzarin da zai kyautata mana wadannan lamura namu. Har ila yau, akwai bukatar mu inganta hanyoyinmu, domin yin gogayya da kasashen duniya,” in ji shi.
Wakazalika, Shugaba na NAHCON ya bukaci kwamitin ya mayar da hankali wajen gudanar da ayyukan da aka ba shi, yana mai nanata musu cewa, aikin nasu na da matukar muhimmanci; don haka dole su mayar da hankali wajen yin abubuwan da suka dace, domin kyautata lamuran da suka shafi abincin alhazai da kuma masaukinsu a hajjin 2024 da ke tafe.
Yayin da yake nuna kwarin guiwarsa na cewa, kwamitin gabatar da shawarwari masu nagarta wadanda za a amfana da su, Arabi ya shaida cewa, kwamitin na da damar fadada ayyukansu ta yadda za su kawo shawarwari masu alfanu da ma’ana.
Idan ba a manta ba, a shekarar 2023 yayin gudanar da aikin hajji a kasa mai tsarki, Alhazan Nijeriya sun yi ta faman korafin matsalar masauki da ba su abinci mara inganci, wanda suka danganta hakan da kamfanin da aka dora wa alhakin ba su abincin da samar musu da masaukai.