Hukumar Kula Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta umarci hukumomin aikin hajji na jihohi su fara amsar naira miliyan 4.5 daga hannun maniyyata a matsayin kudin ajiyar aikin hajjin badi, 2024.
Da yake bayani bayan kammala taro da sakatarorin hukumomin aikin hajji na ji-hohi a hedikwatar hukumar da ke Abuja, shugaban hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan ya ce kudin tafiya aikin hajji na shekara mai zuwa zai kasance da tsada sakamakon daidaita farashin dala da gwamnatin tarayya ta yi, sai dai kuma ya kara jaddada cewa kudin ajiyar na iya canzawa wannan kuma ya danganta ne kan yadda darajar naira ta kasance nan gaba.
- Sakon Shugaban Kasar Sin Ya Nuna Makomar Aikin Raya Tattalin Arziki Mai Alaka Da Fasahohin Zamani
- Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Da Jam’iyyar APM Ta Shigar Kan Ingancin Shettima
Maniyyata aikin hajji na shekarar 2023 sun biya naira miliyan 2.8, hakan ta kasance ne saboda a lokacin ana sayar da kowacce dala daya kan naira 450.
Ya ce, “Kamar yadda muke magana a yanzu, ana sayar da kowacce dalar Amurka daya kan naira 740. Don haka idan ka lissafa kan yadda aka sayar da dala a hajjin bara, yi tunanin miliyoyin da kake bukata a kudin aikin hajji a shekarar 2024. Lallai a yi shiri sosai domin kudin aikin hajjin 2024 zai yi tsada,” in ji shi.
Ya kara da cewa idan har farashin canji ya ragu, farashin kudin aikin hajjin zai ra-gu, idan kuma farashin canjin kudi ya karu, to dole ne kudin aikin hajji ya karu.
Shugaban hukumar NAHCON ya sanar da cewa Masarautar Saudiyya ta fitar da kalandar aikin hajjin 2024, inda ya kara da cewa nan da ranar 29 ga watan Afrilun shekarar 2024 za a rufe bayar da bizar aikin hajji, yayin da ya rage kwana 10 alhazai su fara isa kasa mai tsarki domin gudanar da ibada.
Ya kara da cewa, sabanin yadda ake yi a baya, zuwa aikin hajji na gaba, ma-hukuntan Saudiyya na son sanin adadin maniyyatan da ke zuwa daga kowace kasa kwana 40 zuwa 50 kafin Arafat.
Da ya dauko batun ayyukan hajjin 2023, Hassan ya sanar da cewa hukumar ta samu nasarori duk da wasu kalubale da ta fuskanta.
A cewarsa, a karon farko tun shekarar 2013, hukumar ta samu damar jigilar duk-kan alhazan Nijeriya sama da 90,000 da suka yi rajista kuma aka ba su biza.
Ya sanar da cewa an shafe kwanaki 28 don jigilar alhazai zuwa Saudiyya, yayin da aka kwashe kwanaki ana dawo da su daga kasar.
Da yake magana kan kalubalen da mahajjata suka samu a garin Muna, ya ce NA-HCON ta kafa kwamiti tun kafin kammala aikin hajjin 2023, tare da rubuta wa hukumomin Saudiyya wasikar mayar musu da kudaden da suka biya, sannan ku-ma ta nemi gafarar mahajjatan Nijeriya.
“Hajjin 2023 ya zo ya wuce kuma mun samu nasara kan yadda muka samu damar daukar dukkan alhazan da aka ba su biza zuwa kasar Saudiyya.
“2023 ita ce shekarar da za mu iya kai wannan adadi mai yawa zuwa Saudiyya bayan 2013, shekaru 10 da suka gabata. A bana an kai alhazan Nijeriya 95,000 zuwa kasar Saudiyya lafiya.
“Na biyu shi ne, mun rasa wasu alhazai. Allah ya gafarta musu zunubansu ya shi-gar da su Aljannah. Adadin alhazan da muka rasa ba su da yawa, amma muna fa-tan zai ragu.
“Muna kuma sane da cewa akwai kalubale a Muna, musamman saboda wuraren da aka bai wa ‘yan Nijeriya ba su isa ba, sannan an samu karancin abinci.
“An kafa wani kwamiti da zai duba wadannan kura-kuran kuma kafin mu bar Saudiyya mun nemi a mayar mana da kudaden da muka bayar tare da neman gafara.
“Yayin da muke jiran maido da martani, ina so in sanar da ku a wannan matakin cewa an fara shirye-shiryen Hajj 2024,” in ji Hassan.
Jaridar Tribune ta ruwaito cewa alhazan Nijeriya da suka je Saudiyya aikin hajjin 2023 sun biya tsakanin naira miliyan 2.88 zuwa naira miliyan 2.99.