Shugaban Hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya, (NAHCO), Alhaji Ahmad Jalal Arabi, ya bayar da tabbacin cewa ba za su bai wa muhajjatan Nijeriya kunya ba a yayin aikin hajjin bana.
Jalal Arabi, ya ce sun kammala duk wani shiri domin ganin an gudanar da aikin haj-jin bana cikin nasara.
- An Yanka Ta Tashi: Jami’ar Modibbo Adama Ta Kori Dalibi, Ministan Ilimi Ya Ce Bai Koru Ba
- Kishi: ‘Yansanda Sun Cafke Ma’aikacin Lafiya Da Yunkurin Hallaka Ma’aurata A Bauchi
Shugaban ya bayyana haka ne a taron da majalisar koli ta shari’ar Musulunci ta shirya wa malamai a Jihar Kaduna, yana mai cewa hukumarsa ta kafa kwamitoci da dama domin ganin an yi aikin hajjin cikin nasara.
“Muna da tabbacin cewa duk kwamitocin da muka kafa suna aiki babu dare babu rana wajen tabbatar da cewa ba a samu matsala wajen gudanar da aikin hajjin bana, saboda muna zama da kwamitin malamai da sauran bangarorin da za su gudanar da aikin hajji, kuma in sha Allah aikin hajjin bana ba za mu bai wa muhaj-jatan Nijeriya kunya ba,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp