Gobe Laraba 15 ga watan Mayu 2024 ake sa ran Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCN za ta fara aikin jigilar alhazan Nijeriya zuwa kasa mai tsarki domin aikin hajjin wannan shekarar ta 2024.
A kan haka tuni tawagar farko ta jami’an hukumar NAHCON suka isa kasa mai tsarki domin kammala shirye-shiryen tarbar alhazan da zaran sun isa kasa mai tsarki.
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Sansanin Sojoji, Sun Kashe Dakaru 5 A Katsina
- ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 49 A Zamfara
Ana sa ran fara jigilar ne daga Jihar Kebbi inda alhazai 428 za su tashi daga tashar jiragen sama na Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi, babbar birnin Jihar Kebbi.
Bayanin da ya fito daga mataimakiyar jami’ar yada labarai na hukumar NAHCON Hajiya Fatima Sanda Usara ya nuna cewa, ana sa ran mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar aikin hajji za su halarci bikin fara tashin.
Daga nna kuma sauran Miniyyata daga jihohin Nasarawa, Abuja za su tashi daga filin jiragen sama na Abuja.
Hajiya Fatima ta kuma bayyana cewa, ana sa ran kammala jigilar alhazan Nijeriya gaba daya a ranar 10 ga watan Yuni 2024.
Alhazai 65,047 za su yi aikin hajjin bana daga Nijeriya.