Gwamnan Jihar kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya nada ministan shari’a, Abubakar Malami Amirul-Hajj na Hajjin bana a Jihar kebbi.
Tawagar kwamitin kula da aikin Hajj na shekara ta 2022 a Jihar a karkashin jagorancin Amirul-Hajj, babban lauyan gwamnatin tarayya da kuma ministan shari’a Abubakar Malami SAN, sun gana a sakatariyar hukumar jin dadin alhazai da ke Birnin Kebbi.
Kwamitinn Amirul-Hajj din dai, sun tattauna da masu ruwa da tsaki da ma’aikatan hukumar jin dadin alhazai ta jiha karkashin jagorancin Shugaban Hukumar Alhaji Haruna Abubakar
A wajen taron tattaunawar, an gabatar da muhimman batutuwa kan yadda za a tabbatar da samun nasarar ayyukan Hajji na shekara ta 2022, yayin zuwan su kasar Saudi Arabiya.
Wakilinmu ya ruwaito cewa” majiyar ta bayyana cewa bayan kammala taron, mambobin kwamitin na Amirul-Hajj da sauran masu ruwa da tsaki sun zagaya da kuma ganawa da maniyyatan da aka kira a sansanin alhazai ta Jihar.
A yayin ziyarar, Amirul-Hajj da shugaban tawagar sun tabbatar wa maniyyatan cewa zuwa ranar lahadi za a fara jigilar su zuwa kasar Saudi Arabiya don gudanar da aikin Hajj na bana, inji majiyarmu”.
Bagu da kari, majiyar ta kara da cewa” sawun farko na maniyatan Jihar dari hudu da Talatin ne wadanda suka fito daga kananan hukumomin Bagudo, Jega da Dandi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp