Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Adamawa, ta kwashe kashin farko na maniyyata 475 daga jihar zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2023.
Alhazan da suka tashi a filin jirgin sama na Yola jiya da karfe 8:00 na dare sun fito ne daga kananan hukumomin Madagali, Michika da Girei na jihar.
Malam Abubakar Salihu, Babban Sakataren Hukumar, ya ce Gwamna Ahmadu Fintiri ya samar da dakunan kwana na wucin gadi ga maniyyata a Otal din Meridian da motocin bas guda uku don kai su filin jirgin kafin a dauke su zuwa kasa mai tsarki.
Salihu, ya ba da tabbacin cewa kamfanin jirgin da aka amince da shi (Aero) za su kwashe dukkan maniyyatan cikin lokaci.
Mahajjata 2,574 ne ake sa ran za su gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023 daga jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp