Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Abuja, ya shirya bikin bankwana ga mahajjatan Nijeriya da za su halarci aikin Hajjin 2024.
Ambasada Faisal Ibrahim al-Ghamidy ne, ya jagoranci bikin wanda manyan jami’ai daban-daban, manyan baki, da kuma wasu mahajjatan da suka halarci taron.
- An Kaddamar Da Gwajin Tsarin Binciken Kayayyaki Masu Lambar Kira Na Sin Da Afirka
- Ƴan Matanci A Zamanin Nan
Ambasada Al-Ghamidy ya jaddada kokarin da Saudiyya ke yi wajen samar da ingantacciyar hanyar don kyautata aikin Hajji.
Jakadan ya jinjina wa Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed Bin Salman bisa jajircewarsu na shawo kan kalubalen da mahajjata ke fuskanta.
Ya yi karin haske game da tsare-tsare da saka hannun jari da Saudiyya ta yi don tallafa wa miliyoyin musulmin da ke shiga kasar domin gudanar da aikin Hajji.
An kammala bikin tare da gabatar da kyaututtuka ga bakin Nijeriya, bakin sun jinjina wa masarautar Saudiyya kan irin kulawar da ta ke bai wa Nijeriya.
A wannan shekara, mahajjatan Nijeriya 30 ne, za su shiga cikin shirin baki na masu kula da masallatai biyu, wani shiri da aka tsara don bayar da kulawa da ayyuka na musamman ga mahajjata daga sassan duniya.
Shirin wani tsari ne mai daraja wanda a kowace shekara yake daukar nauyin mahajjata daga kasashe daban-daban, wanda zai ba su damar gudanar da aikin Hajji tare da taimako daga Masarautar Saudiyya don taimaka wa al’ummar musulmin duniya.