Ma’aikatar lafiya ta kasar Saudiyya ta amince wa hukumar alhazai ta Nijeriya NAHCON, gudanar da wasu manyan asibitoci guda biyu na maniyyatan Nijeriya a birnin Makkah.
Shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Arabi, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta hukumar, Fatima Sanda-Usara, ta fitar ranar Lahadi a Abuja.
- NAHCON Ta Karyata Rahoton Bayar Da Abinci Mara Inganci Ga Alhazai A Makkah
- NAHCON Ta Gargadi Alhazai Kan Shiga Da Haramtattun Kayayyaki Saudiyya
Arabi ya ce, Dokta Abubakar Isma’eel, shugaban ofishin kula da lafiya na NAHCON na aikin Hajji na shekarar 2024 ne ya karbi takardar amincewar.
Talla
Arabi ya kuma ce har yanzu ana jiran amincewar fara gudanar da wasu kananan asibitoci guda uku a kasar.
Talla