Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta karyata wasu rahottanin da ke yawo a kafaffen sadarwa na zamani (Shoshiyar Mediya) inda aka bayyana cewa, ana ba wasu Alhazai abinci dan kadan kuma mara inganci a garin Makkah a yayin da Alhazai ke cincinrindo a garin Makkah domin gudanar da aikin Hajjin bana.
Sanarwar haka ta fito ne daga Mataimakiyar Darakta a bangaren watsa labarai, Fatima Sanda Usara a takardar manema labarai da ta sanya wa hannu aka raba wa ‘yan jarida a garin Makkah ranar Talata.
- Hajjin Bana: Kaduna Ta Yi Jigilar Alhazai Fiye Da 1,600 Zuwa Saudiyya
- Falalar Goman Farko Na Watan Zulhajji (3): Kowane Dare Na Kwanakin Daidai Yake Da Lailaitul Kadari
Ta ce labarin da ya samo asali daga shafin Facebook na wani mai suna Babagana Digima inda ya gabatar da hoton wani abinci wanda kamar an ci an rage ne ya ce wai shi ne ake ba alhazai a garin Makkah. “Wannan karya ce tsagwaronta bai kuma kamata a ce manyan jaridu masu mutumci sun yi amfani da irin wannan labari bam, ba tare da sun yi bincike ko kuma sun tuntubi hukumar ba don sanin ciakkken halijn da ake ci.
Ta kara da cewa, mutum na iya tuntubar wani Alhajin garinsu da ya sanu tahowa kasa mai tsari domin sanin irin abincin da ake basu Madina da kuma Makkah, “NAHCON ta tsayu wajen ganin alhazai sun samu kulawar da ya kamata a dukkan zamansu a kasa mai tsari, kofofinmu a bude take ga duk wani mai bukatar sanin halin da ake ciki a dukkan bangarorin tafiyar da aikin hajji ya zo mu sanar da shi, ta kuma nemi ‘yan jarida su guji daukar labarai ba daga ingantaccen kafa ba.