Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya isa filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello na Jihar Kebbi, domin kaddamar da jirgin farko na aikin hajjin 2024.
Maniyyata 430 ne dai aka shirya yin jigilar su ta farko zuwa kasar Saudiyya.
- Emefiele Ya Ki Amincewa Da Tuhumar Da Ake Masa A Kotu
- An Kashe Kasurgumin Dan Bindiga Modi Da Yaransa 4 A Katsina
Haka Kuma jimillar maniyyata 65,500 da suka yi rajista a fadin kasar nan da hukumar jin dadin alhazai da kuma masu gudanar da yawon bude ido da ake sa ran za su yi aikin hajjin bana.
A yayin da Shettima ya sauka a filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi ya samu tarba daga Gwamna Nasir Idris na jihar da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III da Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), Malam Jalal Arabi.
Sauran sun hada da Sanata Ali Ndume, tsohon Gwamna Sa’idu Dakingari na Kebbi, wanda shi ne Amirul Hajji na jihar, Sanata Abubakar Sani, Sanata Bala Ibn Na’Allah, Ministan Ilimi, Alhaji Yusuf Sununu da dai sauransu.
Tuni dai kamfanin Flynas na kasar Saudiyya da aka tanada, kuma daya daga cikin jiragen sama guda uku da aka zaba domin gudanar da jigilar alhazai na 2024, ya kasance a filin jirgin saman, yana shirin fara jigilar maniyyatan.
Arabi, ya sauka ne domin duba jirgin tare da Kwamishinonin dindindin guda uku da Kwamishinansa da ke wakiltar Arewa maso Yamma.
Haka kuma a cikin tawagar akwai ‘yan kadan daga cikin ma’aikatan hukumar NAHCON.
Tawagar FlyNas a wajen ziyarar ta samu jagorancin Malam Umar Kaila, wakilin FlyNas a Nijeriya.
Arabi, ya shawarci masu kula da filin jirgin da su samar da karin matakalar hawa zuwa kofar bayan jirgin domin saukaka shiga cikin gaggawa.
Jirgin na flynas, jirgin zamani mai dauke da kujeru 436, an shirya zai tashi daga filin jirgin ne tsakanin karfe 12 na dare zuwa 1 na rana.
Jirage uku ne aka shirya tashi daga Nijeriya zuwa Saudiyya a ranar Laraba, Air Peace zai tashi daga Abuja tare da alhazan birnin tarayya 310 da jami’ai biyar.