Wani Malamin addinin musulunci daga jihar Gombe a Nijeriya, Sheikh Abdur-Rahman Maigona, ya rasu a kasar Saudiyya sa’ilin da yake aikin hajjin bana a can.
Malamin dan asalin jihar Gombe ya rasu ne a otal din Namma Mawadda da ke birnin Makkah kwanaki kalilan bayan kammala ibadar aikin hajjin bana.
- Jam’iyyar APC Ta Rusa Kungiyoyin Yakin Zaben ‘Yan Takara
- Zaben Musulmai 2: Za A Janyo Rabuwar Kai A Kaduna- Jigo A PDP
An ce ya yi korafin rashin lafiya gabanin ya rasu.
Kamar yadda ganau suka shaida, malamin ya yi kalmar shahada a lokacin da ke gargarar mutuwa.
Malaman addini Musulunci dai sun tafi a kan cewa dukkanin muminin da ya rasu yana kalmar shahada ana kyautata masa zaton ya yi kyakkyawan karshe kuma zai samu rahamar Allah.
Wakilinmu ya nakalto mana cewa an dauki gawar mamacin Sheikh Maigona zuwa masallacin Harami, inda aka masa jana’iza bayan sallar Juma’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp