Akalla mahajjatan kasar Jordan 14 ne suka mutu sakamakon tsananin zafi a kasar Saudiyya, kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.
Ministan harkokin wajen kasar Jordan ne, ya bayyana cewa hakan cikin wata sanarwa.
- Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Sama Da 80 A Katsina
- Me Ya Sa Kamfanonin Waje Ke Neman Ci Gaba A Kasar Sin
“14 daga cikin ‘yan kasarmu sun mutu sakamakon yanayin zafi wanda ya kasance mai muni mutuka.”
Ministan ya kuma bayyana cewa har yanzu mutane 17 ba a san inda suke ba.
Sanarwar ta kuma ce ana ci gaba da kokarin gano mutanen da suka bata.
Bugu da kari, kamfanin dillancin labarai na AFP da kungiyar agaji ta Iran sun tabbatar da mutuwar wasu ‘yan Iran biyar, ko da yake ba a bayyana halin da suke ciki ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp