Raudar Manzon Allah (SAW) na daya daga cikin wuraren da duk wanda ya ziyarci garin Madina yake shaukin zuwa don gabatar da addu’o’i, domin ingattacen bayani ya nuna cewa, Rauda na daga wani yanki na aljanna. A shekarun baya ziyartar Rauda wani abu ne da bashi da wahala kuma babu shamaki, duk lokacin da mutum ya shirya sai akwai ya nufi haramin Manzo (SAW), ya shiga Rauda domin gabatar da addu’oinsa.
Amma a wani sabon salo da hukuma kasar Saudi Arabiya ta bullo da shi a ‘yan shekarun nan, duk wanda ke bukatar ya ziyarci Rauda sai ya yi rajista ta intanet ta wani “application mai suna NSUK’ da aka tanada domin su mahukunta su tsara yadda Alhazai za su shiga su gabatar da addo’insu ba tare da cunkoso ba.
Alhazai da dama da wakilinmu ya tattauna da su sun nuna jin dadi da godiya a kan wannan tsarin. Alhaji Bello Bala daga Jihar Kaduna ya ce, tsarin na da kyau domin a yanzu Alhaji ba shi da wata fargaba, in lokacinsa na ziyarar ya yi sai kawai ya nufi Rauda ya shiga ya gabatar da dukkan addu’o’insa da ibadunsa ba tare da wata matsala ba.
A kan haka ya yi kira ga shugabannin Alhazai su jagoranci alhazai wajen yi musu rajistar shiga Rauda in ba haka sai mutum ya gama zamansa na Madina amma bai samu damar shiga Raudar ba.