Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar Alhamis din nan sun nuna cewa, yawan kayayyakin masarufi da kasar Sin ta sayar a watan Mayu, ya karu da kashi 12.7 cikin 100, idan aka kwatanta da makamancin lokaci na bara.
Bugu da kari, bayanai sun nuna cewa, yawan kayayyakin masana’antun da kasar ta samar, wani muhimmin ma’aunin tattalin arziki, ya karu da kashi 3.5 cikin 100 a watan na Mayu, bisa makamancin lokaci na bara. (Ibrahim Yaya)