Alkalin babban kotun tarayya da ke zamanta a Illorin ta jihar Kwara, Mai Shari’a Muhammed Sani ya yi daurin zaman gidan yari shekara biyar ga wani dan kasar China mai shekara 29 a duniya, Gang Deng, bisa kamasa da laifin hakar Ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) reshen Illorin ce ta cafke Gang a kan hanyar Tsaragi da ke yankin Share a karamar hukumar Edu ta jihar a ranar 9 ga watan Satumban 2022.
An kama shi ne dauke da Tan 25 na danyen Ma’adinai da ake kyautata zaton Lepidolite ne. Ita dai Lepidolite danyen Ma’adinai ne da aka saba kaiwa zuwa Sin domin hada Batirin motoci, wayar salula, kyameta da sauran na’urorin lantarki.
Idan za ku tuna dai hukumar EFCC da hadin guiwar Jami’an Tsaron farin kaya ta NSCDC da ma’aikatar kula da harkokin Ma’adinai ta tarayya a ranar 30 ga watan Agustan 2022 sun gurfanar da mutum 13 bisa zarginsu da hakar Ma’adinai ta barauniyar hanya a kauyen Kakafu da ke karamar hukumar Patigi a jihar.
Dan China din wanda manajan gudanarwa na kamfanin Sinuo Xinyang Nigeria Ltd, ya amsa da kansa cewa yana gudanar da aikin nasa ne ba tare da izinin ba wato lasisi.
Kan hakan ne EFCC ta gurfanar da Gang tare da kamfaninsa a gaban kotun bisa tuhuma guda daya.
A lokacin da aka kira karar, Gang ya amsa laifinsa amma ya ce kamfaninsa ba ta aikata laifi ba.
An dai tuhumesa ne da kwasan Ma’adinai tan 25 da kudinsa ya kai N2,490,000.00 a wata babbar mota DAF mai lamba KLRAD85XCOE603462 wanda hakan ya saba wa sashin doka 1 (8) (b) na dokar laifuka ta MOA ta shekarar 1984.
Alkalin kotun dai ya daure dan China din shekara biyar ko zabin biyan tara miliyan 1.