Hukumar jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON) ta tabbatar da mutuwar mahajjacin Nijeriya a Makka da ke cikin Kasar Saudiyya.
Haka kuma ta bayyana cewa wasu mahajjaci guda daya ya bace a Madina, yayin da wasu mata guda uku suka yi barin ciki sakamakon wasu dadidai.
Shugaban tawagar likitocin hukumar, Dakta Usman Galadima shi ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da manema labarai. Ya ce likitoci guda shida na NAHCON ne ke duba majiyyatan Nijeriya 11,000 da suka samu raunika tun daga ranar da aka fara jigilar mahajjatan.
Hukumar NAHCON ta bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da aka fi samun yawan mata masu juna biyu da suka isa kasa mai tsarki.
Hakazalika, Hukumar NAHCON ta nuna rashin jin dadinta kan zargin da wasu hukumomin aikin hajji na jihohin kasar suka yi mata kan gazawar tura kudi a cikin asusun gata na maniyyata masu aikin hajji bana wanda hakan ne ya sa wasu maniyyatan ba su samu damar tashi zuwa kasar Saudiyya ba domin sauke faradi.
Mataimakin Darakantan samar da bayanai na NAHCON, Mousa Ubandawaki ne ya karyarta zargin hukumomin na jihohin a cikin sanarwar da ya fitar, inda sanarwar ta danganta zargin a matsayin marar tushe balle makama da da ake yi mata.
A cewar Ubandawaki, tun da farko hukumar ta amince da hukomomin kan cewa, kujerun da za a kebe wa maniyya za su kasance daga kashi 60 zuwa 40 a karkashin shirin na asusun gata na ajiyar kudin maniyyatan.
NAHCON ta nuna rashin jin dadinta kan zargin kin samarwa da maniyyan kujerun aikin hajjin bana a karkashina susun gata, inda hakan ya sa wasu hukumin aikin ajji na jihohin Kaduna, Abuja, Gombe da Jigawa suka zargi NAHCON.
Ubandawaki ya kara da cewa, yana da kyau a sanar da cewa Bakin Jaiz ya tura kudaden a cikin asusun gata na maniyyatan ga hukumomin aikin hajji na kasa don gudanar da aikin hajjin na bana.
Ya sanar da cewa, bisa wannan ana jiran hukumar aikin hajji ta Jihar Kaduna ta kebe kashi 40 a cikin dari wanda ya kai Naira 2,000 a cikin asusun gata na shirin.
Ubandawaki ya cewa, duk da wannan adadin maniyyatan, 108 kacal ne aka sanya su a cikin asusun gatan na Jihar Kaduna daga cikin maniyyata 6,255.
Acewarsa, duk irin wadannan matsalolin ne suka faru a sauran hukomomin aikin hajji da ke a sauran jihohin kasar nan, inda suka kitsa hakan don su bata wa NAHCON da shirin na asusun gata suna.
Ubandawaki ya baayyana cewa, hukmar ta ci gaba da nuna yin hakuri da fahimtar su kan shirin da kuma tsarin kafin kwalliya ta fara biya kudin Sabulu.
Ya sanar da cewa, bayanan da hukumar aikin hajji ta Jihar Kaduna ta sanar da sauran takwarorin na jihohi bisa zargin NAHCON karya ce tsagwaronta kuma sun yi hakan ne da nufin bata wa NAHCON suna.
NAHCON ta gode wa wadanda suka shiga cikin shirin na asusun gata, musamman kan yakinin da yardar da suka nuna kan shirin, inda hukumar ta kuma roki maniyyatan da ba a samu damar kwashe su zuwa Saudiyya ba, da su kwantar da hankulan su kuma zamo masu bin doka da oda.