Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta bayyana cewa Nijeriya na bukatar ban-daki miliyan 3.9, domin hana bahaya a fili nan da shekara ta 2025.
Babbar jami’ar tsaftace ruwa ta UNICEF, Misis Jane Beban ita ce ta bayyana haka lokacin da aka bude taron kwana biyu da ya shafi al’amuran masu sana’ar ban-daki a Abuja.
Misis Beban ta bayyana cewa yawan ban-dakin da ake ginawa kowace shekara tsakanin 180,000 zuwa 200,000 matsayin wadanda ba su isa ba.
Ta ce taron an yi shi ne lokacin da ya dace domin kuwa sana’ar gina ban-daki wata hanya ce ta kawo karshen matsalar da ake fuskanta a Nijeriya ta yin kashi a fili.
Ta ce kungiyoyi masu zaman kansu suna da gudunmawar da za su taka wajen ingantuwa da karfafa al’amauran tsafta a Nijeriya.
Beban ta kara jaddada cewa a shekarar 2021 karkashin tsarin WASH ko tsaftace ruwa an gano cewa mutane miliyan 48 ne suke bahaya a fili ba tare da suna da hanyar da za su tsaftace kansu ba, yayin da miliyan 95 ba su da wata hanya ta kusanta da al’amarin da ya shafi tsaftar kansu ko muhalli.
“Ana asarar kashi 1.3 ko Naira biliyan 455 kowace shekara saboda rashin samun ingantaccen al’amarin da ya shafi tsafta da kula da lafiya da yin abin da zai samar da karuwa a gaba.
“Kowace dala guda da aka zuba a harkar da ta shafi ruwa da tsafta za ta samar da dala 3 zuwa 34.
“Nijeriya ba za ta ci gaba da tafiya da al’amura ba tare da abin da gaba za ta iya haifarwa ba, idan ba haka ba tana iya rasa cimma muradan ci gaba na shekarar 2025 ko 2030. Akwai bukatar daukar dukkan matakan da suka dace domin samun damar cimma muradun karni.
“Kungiyoyi masu zaman kansu akwai bukatar su yi aiki kafada- kafada da gwamnatocin tarayya, jihohi, kananan hukumomi tare da kuma gundumomi domin samun damar zuba jari a tsarin ma’aikata”.
Babban Sakatariyar ta ma’aikatar albarkatun ruwa, Didi Walson-Jack ta nuna cewa da akwai tabbacin masu sana’ar ban-daki za su taimaka wa kokarin da gwamnati take yi na cimma muradun hana bahaya a fili.
Ta kara jaddada cewa Nijeriya a shirye take wajen shiga harkar duk da yake akwai tsada idan har ana bukatar samun babbar riba.