Babban kodinaita na gamayyar kungiyoyin arewa na Jihar Katsina, Habibu Ruma ya bayyana wasu hanyoyi da suke ganin idan gwamnatin Jihar Katsina ta yi amfani da su za a iya samun nasara kan matsalar tsaron da ta addibi jihar da yankin arewa baki daya.
Kodinaitan gamayyar kungiyoyin ya yi wannan karin haske ne a lokacin da suka shirya wani taro domin fadakar da ‘ya‘yan kungiyar halin da yanayin da tsaro ya samu kanshi a Jihar Katsina da kuma arewa baki daya.
- Matsayar Ƙungiyar Sarakunan Arewa A Tsaya Kan Umarnin Kotu Kan Rikicin Sarki 2 A Kano
- Mun Dukafa Kawo Karshen Matsalar Wuta A Arewa Maso Gabas – Gwamna Inuwa
Habibu wanda ya yi bitar cewa matsalar tsaro a Jihar Katsina da kuma arewacin Nijeriya ta kassara duk wani ci gaba a bangaren ilimi da haifar da jahilci da rashin shugabanci da shan miyagun kwayoyi wanda har gobe sune ake gani matsayin dalilin faruwar haka.
Yana mai cewa farmakin da ‘yan bindiga suka kai wa sojojin Nijeriya a karamar hukumar Faskari wanda suka kashe sojoji 5 da raunata da dama, sannan kasa da awa 24 aka sake kai wani harin a garin ‘yar Malamai duk a Faskari tare da sace mutum fiye da mutane 80 da sace kayayyakin shaguna da kone gidaje abin takaici ne da zub da hawaye.
Ya bayyana cewa duk da irin kokarin da gwamnatin Jihar Katsina ta yi karkashin gwamna Malam Dikko Umar Radda, musamman samar da dakurun tsaro na C-Watch, sannan an samar da irinsa a Zamfara wato Askarawa da Sakkwato ya kara nuna yadda ake so a shawo kan wannan matsala.
Sai dai ya yi bayanin cewa gamayyar kungiyoyin arewa da sauran kungiyoyin farar hula a Jihar Katsina suna kira da a yi amfani da sabbin hanyoyin sulhu tare da kara samar da wasu hanyoyi saboda yanayin da ake ciki yana bukatar hannu da yawa.
Haka kuma Habibu ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi kokari wajen sanya kowa cikin wannan al’amari domin samun nasara, ba wai ta rika tunzura ‘yan bindiga ba, kamar yadda ake gani a halin yanzu.