Abokai, na taba fada muku cewa, na zo ne daga lardin Hunan, wurin da masanan aikin gona suka fara nazarin inganta samar da irin shinkafa ta hanyar aure, karkashin jagorancin marigayi Yuan Longping, wanda aka yi masa lakabi da “Gwanin tagwaita irin shinkafa” na Sin. Bayan kokarin da suka yi a cikin dadadden lokaci, an inganta irin shimkafa ta hanyar aure, abin da ya magance matsalar karancin abinci a nan kasar Sin.
Baya ga wannan kuma, kwanan baya, kwamitin kolin jam’iyyar JKS, ya gabatar da kundin koli na farko na shekarar 2023, inda a karon farko aka gabatar da ra’ayin inganta karfin kasar ta hanyar raya aikin gona.
Noma tushen arziki. Kaza lika Sin ba za ta samu bunkasuwar a zo a gani ba, idan aka bar sha’anin noma cikin halin koma baya.
Marigayi shehun malami Yuan Longping, ya taba fadawa manema labarai cewa, yana da burika biyu. Na daya irin shinkafa da ya inganta a sabon mataki ya samar da girbi mai armashi. Na biyu kuma, nazarin da tawagar sa take yi ya taimakawa al’ummar duniya baki daya.
Burinsa ya cika, inda aka yayata fasahar inganta irin shinkafa ta hanyar aure, zuwa kasashe da yankuna fiye da 60 ciki hadda Amurka. Alal misali, a Najeriya, yawan shinkafar da aka girba daga irin da aka shigar daga Sin ya karu da kashi 25% bisa na baya a gonan gwaji, matakin da ya bayyana cewa, hanyar da Sin take bi wajen inganta karfin kasar, wajen dogaro da aikin gona, ba ma kawai zai amfani kasar Sin ba ne, har ma zai taimaka wajen daidaita matsalar karancin abinci a duniya.
Mu Bil Adama, makomarmu daya ne, kuma bunkasuwar Sin za ta taka rawar gani ga bunkasuwar duniya baki daya, kuma Sin za ta kara hadin kai da kasashe daban-daban, bisa ra’ayin hakuri da juna, da kawo moriyar juna don samun bunkasuwa tare. (Mai zana da rubuta: MINA)