Kwanan nan ne aka kaddamar da wata babbar hanyar mota, wadda ta tashi daga gabashi zuwa yammacin kasar Aljeriya, wadda kamfanin kasar Sin ya shimfida. Hanya ce da ta samu babban yabo daga al’ummar wurin, kana kyakkyawan abun misali ce ga hadin-gwiwar Sin da Aljeriya, har ma da Sin da Afirka, a fannin raya shawarar “ziri daya da hanya daya”.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin, ya bayyana a yau Litinin cewa, kasarsa na fatan yin kokari tare da kasar Aljeriya, da ma sauran kasashe, wajen kara bunkasa shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta yadda za’a taimaka ga farfado da tattalin arziki, gami da ci gaban duniya mai dorewa.
A shekaranjiya Asabar ne kamfanin gine-gine na kasar Sin CITIC ya mika sashen karshe na aikin ginin babbar hanyar mota da ta hade sassan larduna 17 dake kasar Aljeriya. Karkashin babban aikin ginin hanyar, CITIC ya kammala ginin kilomita 84 na hanyar.
Hanyar wadda ta hade sassan gabashi da yammacin kasar, ta dangana daga birnin Drean na lardin El Tarf a gabas mai nisa, zuwa birnin Raml Souk mai iyaka da kasar Tunisiya.
Yayin bikin kaddamar da sashen karshe na wannan katafaren aiki a birnin El Tarf, firaministan Aljeriya Aymen Benabderrahmane ya jinjinawa muhimmin matsayin wannan aiki, wanda ya ce zai saukaka zirga-zirgar matafiya, ta bunkasa hada-hadar tattalin arziki tsakanin al’ummun Aljeriya da na Tunisiya.
Benabderrahmane ya kuma yabi ingancin aikin hanyar, yana mai cewa, injiniyoyin kasar Aljeriya, da ’yan kwadago da suka shiga aka dama da su a aikin, sun samu karin kwarewa da sanin makamar aiki.
Yayin bikin kaddamarwar, mataimakin babban manajan kamfanin CITIC a kasar Aljeriya Qi Shujie, ya ce injiniyoyin kasar Sin sun fuskanci manyan kalubale yayin da suke gudanar da aikin, ciki har da bukatar gudanar da ciko mai tarin yawa, da matsalar zaftarewar kasa, tun fara aikin ginin kilomita 84 na shekarar 2017, amma duk da haka, sun kai ga kammala aikin a kan lokaci.
Bugu da kari, a wajen taron manema labarai da aka yi a yau Litinin, Wang ya kuma maida martani game da harin da aka kai wa wasu injiniyoyin kasar Sin dake tashar jiragen ruwa ta Gwadar a kasar Pakistan, yana mai cewa, kasar Sin na matukar Allah wadai da irin wannan harin ta’addanci, ta kuma bukaci Pakistan da ta yanke hukunci mai tsanani kan wadanda suka aikata wannan ta’asa, tare kuma da daukar matakan da suka wajaba, don tabbatar da tsaron mutanen Sin dake wajen. (Saminu Alhassan, Murtala Zhang)