Yana daga cikin dabi’u na mata, neman hanyar da za su mallaki miji. Irin wannan lamari kan ba wasu mata matsala wajen gane yadda za su bi su mallaki miji cikin sauki. Wasu daga ciki gani suke, zuwa wurin boka ko malam a samu wasu siddabaru a matsayin taimako domin mallake miji shi ya fi sauki, yayin da wasu su kan dace a hakan, wasu kuma akasin haka ne.
Ga wadanda suka yi dace siddabarun ya yi masu amfani, zuwa wani dan lokaci kalilan zai daina amfani a koma kiyayya.
Mata ga hanya mafi sauwi wajen mallakar miji wanda aka tsara bisa koyarwa manzo. Kamar yadda maluma na addini ke nasiha da tuni kan cewa, Aljannar mace na karkashin kafar mijinta. Kawai ki dukufa kan wadannan ababe da ma wasu don mallakar miji cikin sauki:
1- Ya kasance duk maganar da za ta fita daga bakinki mai dadi ce a kunnen mijinki wanda zai sa shi murmushi da jin dadi. 2- Ki kasance mai sakin fuska ga mijinki a duk lokacin da ya shigo gida ya same ki cikin farin ciki.
3 – Ki kasance a kullum kin dokin mijinki tamkar sarki ne ta wurin mutunta shi, da juriya wajen daukar laifinsa ya dawo kanki saboda bashi girma ko da ke ce da gaskiya.
4 – Kar ki kasance kullum a cikin bacin rai ko fushi da mijinki, domin fushi kofa ce ta kowane sharri.
5 – Kar ki kasance mai girman kai wajen bashi hakkokin zamanku, abin da yake so ko da baki so matukar bai saba wa addini ba ki yi masa.
6 Ki nuna wa mijinki komai naki nasa ne komai nasa kuma nasa ne, ki nuna baki da iko a kai sai abin da ya yi.
7- Ki kasance mai kula da abubuwan da yake dubawa a jikinki in ya shigo gida, ina idonsa ke kallo a jikinki. Bayan kin yi kwalliya. sai a gyara masa su da kyau domin a dauke masa hankali. In kuma kin tabbatar duk lokacin da ya dawo yana neman buta ne, to ki kula da sanya ruwa a cikin butar.
8 – Ki kasan ce mai yawan godiya kan duk abin da ya kawo miki gida komai kankantar abin kar ki raina, sannan ki nuna masa kokarinsa a kan bin da ya kawo.
9 – Kar ki sake ko ki yi kasa a gwiwa wajen girmama duk wadanda kika san yana girmama su, kama daga iyaye har ‘yan uwa da abokan arzikinsa.
10- Kar ki yawaita tambayarsa daga ina kake ko me kake yi sai yanzu kake dawowa?
Ki kasance mai boye sirrinsa wajen iyayenki da sauran al’umma. 11 – Kar ki yarda duk lokacin da ya kiranki ki kawo masa wani abu ki tura wani ko wata ta kawo, ki je ki yi da kanki. Wadan abubuwa idan kika daure kina yi lallai za ki samu namiji a hannunki kamar dan jariri. Allay a ba da ikon yi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp