Hada-hadar kasauwancin shanu, na daya daga cikin kasuwanci mai riba da ake yi a Nijeriya. Akwai hanyoyi hudu da za a iya samun kudin shiga a sana’ar sayar da shanu baya ga kiwata su. Wadannan hanyoyi guda hudu su ne kamar haka:
Saye da sayar da Shanu:
Ana neman shanu kwarai da gaske a Nijeriya, ana kuma yanka su a kowace rana, musamman a lokacin gudanar da shagulgulan bukukuwa da kuma mayanka. Za a iya samun kudaden shiga masu yawan gaske ta hanyar tura shanu gonaki domin yi musu baye, ana kuma sayen shanu a Arewacin Nijeriya a kai su kudancin wannan kasa a sayar, a kuma samu riba mai tarin yawa.
Kazalika, idan ba a son kai su mayankar yanka dabbobi, za a iya yanka su a rika sayar da naman kilo-kilo ga masu saha’awar saya. Har ila yau kafin a sayo shanu, yana da kyau a gano kasuwar da ake sayar da su wadda ta dace, domin gujewa kashe kudi da yawa kafin a sayar da su.
Bugu da kari, za a iya tattaunawa da kungiyoyi da manyan kamfanoni wadanda ke bukatar saye, domin kai musu har inda suke su saya.
Kashin Shanu:
Wasu masana’antun na bukatar kashin shanu, domin sarrafa su zuwa abincin kajin gidan gona, musamman ganin yadda kashi ke dauke da sinadarin ‘calcium’, wanda kai tsaye ke gina jikin Kaji.
Ana samun kashin shanu a mayankar dabbobi, sannan ana shanya su ne su bushe, kamin a kai ga sayar wa manyan masana’antun da ke sarrafa shi zuwa abincin Kaji.
Haka zalika, za a iya nika kashin shanu a mayar da shi zuwa kilo 50, domin fitar da shi zuwa wasu jihohi ko sauran kasashen ketare a sayar.
Fatar Shanu:
A Nijeriya, ana yi wa fatar shanu lakabi da “Pomo”, wadda wasu ke ci a matsayin nama. Ana kuma yin amfani da fatar shanun wajen sarrafa ta a yi takalma, jakunkuna da sauran makamantansu.
Biyo bayan haramta cin fatar shanu da ake kira da Ganda “Pomo”, hakan ya kara sanya matukar bukatar ta a tsakanin masana’antun da ke sarrafa ta, musamman zuwa wasu nau’ika daban-daban a wannan kasa. Kazalika, ana sarrafa wannan fata ta shanu a kuma fitar da ita zuwa Nahiyar Turai da sauran yankin Asiya.
Kahon Shanu:
Za a iya samun dalolin kudi yayin fitar da kahon shanu zuwa kasashen waje, ana kuma son a tabbatar da kauce wa rubewarsa da kare shi daga wasu ababen da za su iya janyo wa ya rube a jikinsa kafin a sayar wa da masu bukatar sa. sannan, ana sarrafa shi zuwa wasu nau’ikan kaya da suka hada da kofuna, cokula, sarkoki, tebura da sauransu. Kazalika, hada-hadar kasuwancin kahon shanu a Nijeriya, na ci gaba kara fadada da kuma samun tagomashi.