Ci gaba daga makon jiya
10. Samar Da Abubuwan Da Za Su Bada Kwarin gwiwa.
Yana daga cikin abubuwan da aka fi so na lokacin da aka gina makaranta na samar da hanya da zata sa Malamai su kasance babu wani abin da ke damunsau, suna kuma da kwarin gwiwa a wurin aikinsu.
Za a samu mutane masu magana da harsuna mabambanta, su kasance maza da mata daga kasashe daban- daban,al’adunsu ma sun bambanta, da dai sauran abubuwa da suke mabambantansu.Anan kamata ya yi a amince da yadda Malaman suke daga wurare daban- daban.
Idan makaranta ta kasance inda su Malaman suke da dama ta fadar albarkacin bakinsu irin hakan zai sa hankalin su ya kwanta su kara zage damtse wajen aiwatar da ayyukansu.
Alal misali Ellucian wata kafa ce mai samar da lamarin komfuta mai taimakawa ta bangaren ilimi mai zurfi,bugu da kari tana taimakawa wajen ganin ayyukan da suka shafi makarantar sun tafi kamar yadda ya dace.
Ellucian ta shafe fiye da shekaru 40 inda ta maida ilimi mai zurfi shne aikinta wanda ta sa gaba, inda ta nuna lalle ta kware ta wancan bangaren na taimakawa makarantu a fadin duniya.
Kamfanin ko shakka babu ya nuna lamarin haka ne saboda kuwa ya yi mu’amala da makarantu 2,400 a fadin duniya cikin kasashe 40.Wannan shi yasa kowa zai iya gane gudunmawar da Ellucian yake badawa ta bangaren ilimi mai zurfi,na makarantun kasa da kasa.
Al’amarin na Ellucian ya wuce duk yadda wani yake tsammaninsu domin kuwa ya samar da wani tsarin da yake da yanayi wanda duk abubuwan da mutum yake bukata su kwantar ma shi da hankali domin tafiyar da aiki suna anan ba sai an je wani wuri ba.Hakanan ma abin ya nuna lalle bada wasa suke yi ba wajen samar da yanayin da kowa zai ga ai ya samu wurin da zai yi aiki kamar yadda ya dace aka kuma amince da shi.
Kasancewar lamarinEllucian na maida hankali kan ilimi mai zurfi da yayi fice a duniya abin ya kasance hakan ne saboda hankalin da kamfanin ya nuna danagane shi lamarin na ilimi.Yadda kamafanin yam aida hankalin shi wajen samar da kayan aiki da aiwatar da hakan ga su makarantun,shi yasa hakan ta nuna lale maganar d ake yi dangane da aiki tukuru na kamfani ba wasa bane,koba komai ai za a kara bunkasa ilimin yadda ake koyarwa domin cigaban makarantun da al’ummarsu.
11. Lokacin aiki da sharuddan da suka dace a lura da su.
Malamai suna da iyalai da sauran wasu hidimomin da suka rataya kansu da ya kamata su ga cewar sun yi abin da ya dace na samar duk amsa lamarin da yake bukatar daukar mataki. Shi ya sa samar masu hanyoyin gudanar da aikinsu da ke basu dama suma su yi wani abu dangane da lamuran da suka dame su ba tare da tunkarar matsala ba.
Ta daya bangaren kuma idan har Malaman makaranta sharuddan aikinsu akwai matsaloli tattare da su hakan za isa suma su fuskanci matsala wajen gudanar da su, saboda kuwa daga karshe sai abin ya kai ga shafar kafiyarsu.
Irin hakan zai sa su kasance suna a matse basu da nasu lokacin abin da za isa su kasance babu wani kwarin gwiwar da za su samu dangane da aiwatar da aikinsu,babbar mafitar da za a iya kaucewa aukuwar irin hakan bata wuce ayi tsarin aiki wanda ba cuta ba cutarwa.Ya dace a saurari duk wani korafi na Malamai da amincewa da su.
Matukar an yi hakan za su iya gane cewa an damu da su da kuma abubuwan da ake ganin idan ba wani mataki aka dauka ba daga karshe sai an hadu da abinda ba a so.
Alal misali Coursera daya daga cikin jajirtattun masu samar da ilimin fasaha EdTech, abinda suka yi shine ba ma’aikatansu zabi na su bayyana matakan da idan aka dauka za su taimaka masu wajen aiwatar da aiyukansu da cimma buri ba tare da wata matsala ba, sai kowa ya ce gara da aka yi hakan. Babban abin da suka ga yafi dacewa kada lamarin kai Malami wani wurin da shi bako ne ya zama wani karfen kafa da har hakan zai iya shafar aikinsa na yi na gabatar da abubuwa kamar yadda kasashe ko wuraren da suka ci gaba suke yi.
Ta haka ne su Malaman za su kara fahimtar ko shakka babu an amince da su a wuraren da suke aiki hakan shi zai iya kawo ci gaban da kowa zai amfana, saboda sharuddan aikin nasu ba za su sa su yi kasa a gwiwa ba, maimakon haka ma ci gaba za su yi da ba mara da kunya,duk kuwa da yake mai rai baya rasa motsi.