Duk da yake ana ci gaba da samun fasahar zamani ta yanar gizo ko kuma Internet inda ‘yan makaranta suke kara samun ilimi ta bangaren karatunsu,da akwai abu daya wanda zai dade ba a canza shi ba shine irin gudunmwar da Malaman Makaranta suke badawa dora turbar da zata kai su zuwa tudun mun tsira wajen fafutukar da suke yi wajen neman ilimi.
A shekarar 2019 rabin ‘yan makaranta ko dalibai na duniya baki daya tuni suka fara rungumar hanayar zamani ta koyon ilimi ta kafar sadarwa ta zamani ta hanyar yin kwasa- kwasai, saboda a wani binciken da aka yi an gano cewa kashi 80 cikin 100 na daliban kwaleji sun amince da cewar hanyoyin koyon kamar yadda ake yin karatu ta hanyar wayar hannu,maganganu ko hira a aji, ko shakka babu hakan na taimakawa inganta ilimin daliban.
- Kwaskwarimar Kundin Tsarin Mulki Zai Gyara Kura-kuren Da Aka Samu A Zaben 2023 – Abbas
- A Bara Adadin Dalibai Sinawa Dake Karatu A Manyan Makarantu Ya Kai Sama Da Miliyan 47
Sai dai kuma ba Miya za ayi ba a manta da albasa saboda kuwa maganar gaskiya muhimmanci Malami ya fi duk wasu abubuwan da mutum zai iya yin tunani kansu.
Alal misali Malamai yana iya jan hankalin fiye da dalbai 3,000 ta hanyar aikinsu ana Malamta inda yake kasancewa wani abin da suke misali da shi, a duk wani halin da za su shiga ko fuskanta lokacin rayuwarsu ta makaranta da ci gaban da suka samu bayan sun kammala makaranta. Hakanan ma akwai kashi 54 da suke godewa Malamansu yadda za su tafiyar da rayuwa aduk halin da suka samu kansu, yayin da kuma kashi sun yarda da cewa maganar gaskiya ce ba karamar gudunmawa Malamansu suka bad aba wajen sa su hanyar da ta dace wadda ta sa suka gane ko su, su wanene, su kuma amince da cewar babu wanu abin da zai gagare su matsayar sun maida hankalinsu a cikin al’amarin.
Duk wadannan abubuwan sun nuna a gaskiya cewa irin alakar dake tsakanin Malamai da ‘yan makaranta al’amarin ba ya tsaya bane kawai a hanyoyin koyon ilimi ta gargajiyance da kuma zamanance.
Ga abubuwa goma sha biyar wadanda idan aka aiwatar da su za su taimaka wajen bunkasa ko bada kwarin gwiwa ga Malaman makaranta, ko dai suna koyarwa ne a makarantar Firamare, Sakandare, Kwaleji, ko kuma Jami’a.
1. A gode wa Malamai a duk lokacin da suka yi wani abin bajinta
Malaman makaranta sun son idan sun yi wani abin da za a yaba masu to a yaba masun, kamar dai yadda wadanne masu bada aiki ko daukar aiki suke, akwai bukatar a rika godde masu.
Ko dai al’amarin babba ne ko karami na aikin da suka yi ko abin da ya shafi aikinsu, kada amanta gode masu akan gudunmwar da suke badawa.Idan ana nuna gode masu kan ayyukan suke yi wata hanya ce da zata nuna masu cewar ana jin dadin ayyukan alkhairin da suke yi wajen koyawa dalibai ilimi.Ko shakka babu yin hakan zai kara masu karsashi su kara maida himma wajen gudanar da aikin nasu.
Alal misali wato al’amarin da ya shafi koyarwa na LinkedIn Learning yana tunawa da ma’aikatansa duk lokacin da aka tashi yin abin da ya shafi ci gaban Kamfanin,wato irin ta kafar sadarwa ta zamani inda ake rubuta labaran kamfanin,ko ta kafar sadarwar zamani ta kamfanin.