Ana bukatar a gina musu dakin kwana tare da ware su daga cikin sauran tsintsayen da ake kiwatawa a gida.
Har ila yau, ga wadanda suke wannan sana’a ta kiwon zabo, zai taimaka musu matuka wajen samun kudaden shiga masu yawa, har ila yau kuma, macen zabo na zuba kwai sama da 70 kafin ta fara yin kwanci, kazalika, zabo bai cika yin rashin lafiya ba.
Yadda Ake Fara Kiwon Zabi:
Haka zalika, kiwon zabi ba sabon abu ba ne, domin kuwa fanni ne wanda aka jima ana yin sa a fadin Nahiyar Afirka da daukacin fadin duniya baki-daya, musamman don samun riba.
1- Zabar Waje Mai Kyau: Ya na da kyau a samu waje mai kyau tare da tanadar kayan kiwonsu, sannan a tabbatar da samar musu da tsaftataccen ruwan sha. Sannan, idan aka sa musu wutur lantarki; shi ma abu ne mai kyau.
2- Dakin Kwanansu: A nan ma ya na da kyau a sama musu dakin kwana, domin ba su kariya daga zafin rana, buji, sanyi da kuma kare su daga wasu dabbobin da ka iya cutar da su.
3- Zabe Da Sayen Irin Zabin Da Ya Kamata A Kiwata: Bayan sama musu wajen kwana, ya na da kyau a zabo zabi masu inganci da lafiya da za a kiwata, sannan za a iya sayo su a kasuwar da ke kusa ko kuma a saya ta hanyar yanar Gizo.
Bayan an sawo zabin, ya na da kyau a bar su a cikin dakin kwanansu har zuwa akalla sati daya ko biyu, domin su saba da dakin in ba haka ba kuma, suna iya guduwa.
4- Ciyar Da Su Abinci: Baya ga abincin da za a ciyar da su, suna kuma so a bar su a kashin kansu su yi kiwo, don samun abincin da zai gina musu jiki, inda akasari su kan ci kwari iri daban-daban da kuma ciyawa, haka nan suna bukatar cin Alkama, Gero da kuma Rogo.
5- Ana Yin Bayen Su: Kamar sauran tsintaye da ake kiwatawa, su ma zabi ana zuba musu maniyin wani tsuntsun, don samar da wani nau’in tsintsun.
6- Basu Kulawar Da Ta Dace: Zabuwa ba ta cika iya lura da ‘ya’yan da ta haifa ba, domin a wani lokacin su kan yi watsi da ‘ya’yan, saboda haka ana so mai wannan kiwo ya tabbata ya na sa ido sosai, har sai sun fara fitar da gashi
7- Kamuwa Da Cututtuka: Garkuwar jikinsu na da karfi matuka, inda hakan ya ke taimaka musu wajen samun kariya daga saurin kamuwa daga cututtuka da sauran laruran da suka shafi matsalar kiwon lafiya.
Sai dai duk da hakan, ana so mai kiwon ya kasance ya na sa likitan dabbobi ya na duba lafiyarsu.
8- Hada-Hadar Kasuwancinsu:
Hada-hadar kasuwancinsu ba ta da wata wahala, domin tun daga namansu har zuwa kwansu, ana bukatar su matuka a kasuwanni.