Gashi na daga cikin abubuwa da suka fi daukan hankalin namiji a jikin mace. Namiji kan ji farin ciki a yayin da ya kalli ko ya taba gashin uwargidansa musamman idan gashinta ya kasance mai sheki ne tare da laushi sannan kuma baki.
Akwai hanyoyi da dama na gyaran gashi, za mu yi bayaninsu daya bayan daya:
Amfani da tafarnuwa da man zaitun: yanda zakiyi saiki samu tafarnuwan da dan yawa kamar sama da goma sai ki baresu ki yayyanka sannan ki jikasu da man zaitun sai ki bari yayi kwana uku ajike sannan ki soya ki ajiye kina shafawa akan bayan awa daya a wanke.
Amfani da man Amla da man Kwakwa da Zuma:
Yadda ake amfani da shi shi ne; Za ki zuba man Amla kadan zuma ita ma idan Amla ya zama cokali hudu to zuma ya zama cokali biyu man kwakwa shi ma cokali biyu, sai ki zuba a ruwan zafi, shi kuma kamar cokali hudu a gauraya kamar idan za’a yi shampoo sai a shafa a kai bayan mintuna talatin shikenan sai ki yi shampoo dinki.
Amfani da man kwakwa da man Amla: Daga farko ki dora man kwakwa a wuta sannan sai ki zuba masa man Amla. Daga nan sai ki gauraya sosai, idan kin tabbata sun gaurayu, sai ki sauke daga wuta, har hadin ya huce. Sannan ki zuba man a kwalba kina shafa wannan hadin a fatar kanki da gashinki kamar sau uku a sati.
Amfani da Lemon Tsami: Ki samu ruwan Lemun Tsami, sai ki hada shi da kwai da kuma man Amla. Sai ki shafa hadin a fatar kai da kuma gashi. Ki bar hadin a kanki har tsawon minti talatin, sannan ki wanke da ruwan Dumi. Za ki iya yin wannan hadin sau biyu a wata.
Amfani da Alo Bera: Ki samu ruwan Alo Bera, sai ki shafa a fatar kai da kuma gashi, bayan minti ashirin sai ki wanke da ruwan dumi.
Amfani da man Zaitun: Man zaitun na sanya gashi ya yi baki, taushi da kuma tsawo. Za ki iya mayar da man zaitun ya zama man kitsonki.
Hanyoyin karin tsawon gashi
Amfani da danyen kwai:
Kayan hadi:
Danyen Kwai. Roba mai Kyau mai dan fadi
Ki samu wannan kwan naki sai ki dauko wannan roba taki sannan ki fasa wannan kwan sai ki cire kwanduwar kwan ma’ ana wannan yallon abin na ciki ki ajiye gefe daya, sai ki juye farin ruwan kwan a wannan roba taki. Idan gashin naki da dan yawane sai ki fasa kwan kamar uku-kodai yada ya samu. Sannan ki dinga diban wannan farin ruwan kwan kina shafe shi a gashin naki, har sai kin tabbatar cewa ruwan kwan ya ratsa ko ina cikin gashin naki.
Saiki bar shi tsawon mintuna ashirin ko talatin sai ki wanke kan naki da sabulu mai kyau kina iya amfani da sabulun Alo Bera. Kada kimanta cewa gashi ya kan sanya mazaje kara kaunar matayensu .
Amfani da man Amla:
Abubuwan da za a bukata: Man Amla, Zuma, Ruwan dumi. A zuba cokalin Amla biyu a roba, sannan sai a zuba rabin cokalin zuma a cikin Amla, a sanya cokalin ruwan dumi kamar biyu zuwa uku, sannan sai a juya hadin har sai sun cakudu da juna, daga nan a taje gashi kamin a shafa wannan hadin a fatar kai.
A jira na tsawon mintuna talatin, daga nan sai a wanke kai da man wanke gashi (shampoo).
Maganin bushewar gashi
Amfani da ayaba: Kayan hadi : Zuma cokali daya, Nunanniyar Ayaba, za ki bare bawon Ayaba sai ki markada a injin nika (blender ) ta markadu sosai .
Ki zuba zuma cokali daya ki gauraya su su hadu , sannan ki shafa a gashi tun daga karkashinsa har baki. Ki rufe kan da hular leda (shower cap). Bayan mintuna sha biyar zuwa ashirin sai ki wanke kan da sabulun wanke gashi (Shampoo ) da na karawa gashi maiko (conditioner ).
wannan ita ce hanya mafi sauki kuma mafi kawo sakamako mai kyau.
Kwabin Kwanduwar kwai da Fiya (Abocado )
Kayan hadi:
Kwanduwar kwai, Fiya
Ga yadda ake hadawa
Za ki bare Fiya, sai ki zuba a injin markade, ki zuba kwanduwar kwan ki a kai sai ki markada sannan ki shafa a gashinki tun daga karkashin sa har baki. Ki samu hular leda ki rufe kan da shi.
Ap Oil, Man Shafawa
Yadda za ki hada asamu manshafawa mafi kankanta wato mai araha sai a juye kwalbar ap oil gaba daya sai a sami wani abu a juya sosai sai a rufe bakin tsawon minti biyu (2) ko uku ( 3 ) shikenan ya hadu.
Dokokin amfani da shi:
- Mutane 2 Ba sa Tabawa
- Ba a barinsa a bude. Ba a amfani da manshafawa mai tsada sai ( Local One)
- Ba a sawa da rana sai gari ya yi huhu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp