• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Magance Amosanin (Dandruff)

by Bilkisu Tijjani
2 years ago
Magance

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

Hadin Tsumin Baure

Yadda uwargida za ta magance Amosanin kai wato (Dandruff) a saukake wanda yanzu yake addabar mata.

Abubuwa mafi saukin samu:

Abubuwan da za ki bukata su ne : Tumatir, Sabulun Salo, dan kwano ko roba, sai kuma Leda.

Uwargida ga yadda za ki hada:

Da farko dai za ki samu sabulun salonki kamar rabin gwangwanin madara amma ya danganta da yawan gashinki, ki samu tumatur masu kyau wanda suka nuna kamar  guda uku idan manya ne ko hudu haka sun isheki.

Ki zuba sabulun salonki a cikin dan kwano ko roba sannan ki matse iya ruwan tumatur din ban da bayansa, sai ki jujjuya su sosai su hadu sannan ki bashi lokaci domin ya juku so sai za ki iya jika shi da safe idan da daddare za ki yi ki kwana da shi don an fiso ya dauki lokaci sosai a kanki.

Idan kuma ba ki samu ya kwana ba za ki iya amfani da shi duk lokacin da kika samu, kafin ki fara dama kin tsefe kanki kin taje shi so sai, sai ki raba gashinki kamar kashi hudu amma ba haka za ki bar shi ba za ki daure can saman gashin ban da kasansa yadda idan kin saka wannan hadin zai shiga kasan kanki sosai.

Sannan ki dauko wannan hadin tumatir da sabulun salon ki  rika diiba a hankali kina zuba shi a kanki kina mummurza shi sosai domin ya shiga ko ina a cikin kanki musamman kasan gashinki, haka za ki yi ta yi har sai kin tabbatar wannan kaso hudun da kika yi wa gashinki duka sun jiku da wannan hadin, amma ki kula sosai ta yadda ba za ki bata jikinki ba ya zama iya kanki kadai kika shafa wannan hadin, bayan kin gama za ki samu leda mai kyau babba wacce za ta rufe miki kai ta yadda ko iska ba za ta shiga ba, idan kuma kina da shawercap sai ki sa ki dora hularki a kai, saiki bar shi ya yi kamar awa hudu ko biyar idan kuma na daren kika yi wanda shi ne ya fi to, gari na  wayewa sai ki samu ruwan dumi ba mai zafi ba sai ki dauko sauran hadin ki yi amfani da shi wajan wankewa ki murza kanki sosai har sai kin ga ya fitar da kumfa, wajen wankin ki tabbatar duk ‘ya’yan tumatir din sun fita yayin da kike wankewa.

Shikenan sai ki taje shi sosai ki busar da shi tun da zamani ne yanzu uwargida za ki iya amfani da hand dryer wajan busarwa shikenan sai a shafe kai da man gashi. Uwargida wannan ita ce hanya mafi sauki da za ki yi maganin Amosanin Kai.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki
Ado Da Kwalliya

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

October 4, 2025
Hadin Tsumin Baure
Ado Da Kwalliya

Hadin Tsumin Baure

September 27, 2025
Gyaran fuska
Ado Da Kwalliya

Gyaran Fuska Da Laushin Fata

August 30, 2025
Next Post
Sojoji Sun Ragargaji Haramtattun Matatun Mai 30 Da Cafke Mutum 42 Cikin Makonni 3 – DHQ

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 4 Da Ceto Mutum 24 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.