Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da a wannan mako a cikin shirinmu na Ado Da Kwalliya.
A yau shafin namu ya zo muku da yadda za ki Magance Nankarwa:
Da farko dai ita Nankarwa wasu tabbai ne layi-layi da suke fitowa mace a jiki musamman wacce ke dauke da cikin haihuwa wanda idan an yi maganin ta da wuri wato daga fitowar ta za su iya bacewa gaba daya amma barin ta ta dade kan hana ta bacewa gaba daye sai dai zai dusashe ta zama dan kadan-kadan ake iya gani
Suna fitowa ne a wurare kamar haka:
Cikin mace daga kasa wato (mara), cinya, saman mama, mazaunai, saman hannu ta wuraren hammata da sauran su.
Meke kawo Nankarwa?
Akwai abubuwa da dama da suke sa Nankarwa ta fito
Na daya: Daukar ciki zuwa haihuwa (wannan shi ne babban abin da ke kawo Nankarwa). Na biyu; Ramewa tashi daya (ga mutum mai kiba). Na uku; Yin kiba tashi guda (ga mutum mai rama). Na hudu; Gado daga mahaifiya. Na biyar; Jinya ta tsawon lokaci. Na shida; Damuwa mai yawa da makamantan su.
Matakan Nankarwa:
Nankarwa tana da matakai guda uku:
Farkon fitowar su za ki gansu sirara yana da pink kala sannan ya kan yi kaikayi wannan matakin bashi da wahalar magani.
Na biyu, zai zama ja ko ruwan bula sannan girmansu zai karu yanzun kam babu kaikayi sai lokaci zuwa lokaci zai yi kaikayi ya danganta da yanayin jikin mutum
Na uku; Zai zama fari ko ruwan silba wannan kam yana da matukar wahalar magani sai an jure shima din sai dai ya ragu ba wai ya bace baki daya ba.
Hanyoyin Magance Nankarwa:
Ruwa:
Ruwa da Kuke gani ya fi komai mahimmanci a jikin dan’Adam. Rashin shan ruwa yana sa jikin mutum ya bushe ya tattare tare da saurin tsufa a yayin da yawan shan ruwa kofi 8-10 kullum yake sanya taushin jiki da kyawun fata kuma ya hana wasu cututtuka da dama kama fatar mutum da wuri.
Misalin yanda zaki sha kofi 8 zuwa goma acikin ko wacce rana
Kofi biyu da zarar kin gama wanke baki da safe, kofi daya bayan karin kumallo, kofi daya kafin Azahar ki sha. Kofi daya kafin abincin rana daya bayan kin gama ci. Kofi daya da la’asar.
kofi daya kafin abincin.
Ba iya mai juna biyu Nankarwa ke fitowa ba
Abubuwa 10 da suka kamata ki sani game da Nankarwa.
Nankarwa alama ce ta talewar fata, an fi ganinta galibi a tsatstsaye a kan fata, kalar Nankarwa ya dogara ga kalar fatar mutum. 2. Akwai shimfidu uku da suka hadu suka samar da fata. A likitance, Nankarwa na faruwa sakamakon talewar shimfidar fata ta biyu.
3. Galibi ta fi fitowa a kan fatar ciki, sai dai wasu lokutan tana bayyana a kan fatar cinyoyi, maman mace, kugu, da sauransu. 5. Nankarwa aba ce ruwan dare, kuma tana iya fito wa kowa, maza da mata, babba da yaro, ba sai mata masu juna biyu kawai ba.
6. Wadanda suke sabun fitowar Nankarwa sun hada da:
i. juna biyu: Kaso 8 cikin 10 na masu juna biyu Nankarwa na fito musu. ii. wadanda suke cikin shekarun balaga. iii. Wandda ya rame ko ya yi kiba nan da nan. 7. Ga masu juna biyu, Nankarwa na bajewa ko ta tsutstsuke bayan haihuwa. 8. Wasu nau’in mayukan shafawa suna ikirarin magance Nankarwa, sai dai babu kwakkwaran dalilai da suka tabbatar da ikirarin nasu.
9. A likitance, Nankarwa, musamman ga masu juna biyu, ba ta da wata matsala. Sai dai idan akwai kaikayi ko kuma damuwa game da munin da Nankarwar ke haifarwa ga fata, za a iya tuntubar likitan fata.
10. Har wa yau, za ki iya tuntubar likita idan Nankarwa ta yi fadi sosai tare da bayyanar tarin kitse / teba a ciki, wuya da kirji domin hakan na iya zama alamun wata cutar daban.