Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba 9 da 10 ga Afrilu, 2024, a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan Sallar Eid-el-Fitr.
Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ranar Lahadi a Abuja.
- Tinubu Zai Tafi Legas Don Gudanar Da Bikin Sallah
- Maganin Yaki Da Malaria Na Sin Zai Yi Matukar Tallafawa Uganda
Tunji-ojo, a cikin sakon taya murna da babbar sakatariya a ma’aikatar, Dakta Aishetu Gogo Ndayako ta fitar, ta taya al’ummar Musulmin Nijeriya murnar kammala azumin watan Ramadan mai alfarma.
Ministan ya hori al’ummar musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’u da suka hada da kyautatawa, soyayya, hakuri, zaman lafiya, kyakkyawar makwabtaka, tausayi kamar yadda Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya koyar.
Tunji-ojo ya bukaci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da kasancewa cikin ruhin hadin kai domin karfafa zaman lafiya da kuma inganta hadin kai a kasar.
Talla