Ga duk mai bibbiyar manufofin kasar Sin na samun ci gaba, da bunkasa hadin gwiwa da sauran sassan kasa da kasa, ya kwana da sanin cewa har kullum gwamnatin Sin na yayata batun wanzar da zaman lafiya da lumana a dukkanin alakarta da sassan kasa da kasa, inda kasar ke nacewa yayata manufar dakatar da bude wuta, da kawo karshen tashe-tashen hankula a yankuna masu fama da rigingimu.
Ko da a baya bayan nan ma an jiyo wakilin dindindin na kasar a MDD Fu Cong, na kira da a dauki dukkanin matakan da suka wajaba, na kare rayukan mata da matasa yayin da ake fuskantar tashe-tashen hankula, lokacin da yake tsokaci a zaman muhawarar kwamitin tsaron MDD game da wanzar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.
-  ‘Yancin Taiwan Na Nufin Yaki, In Ji Kakakin Ma’aikatar Tsaron Kasar Sin
- Sojojin Nijar Sun Cafke Kasurgumin Dan Bindigar Da Ya Addabi Zamfara
Ko shakka babu, yanzu haka duniya na fuskantar manyan kalubale na barkewar rikice-rikice nan da can, musamman a gabas ta tsakiya, da wasu kasashen Afirka, da Turai, don haka kiraye-kirayen da Sin ke yi a wannan gaba, suna zuwa a kan muhimmin lokaci da ake bukata.
Mun dai san cewa, a duk lokacin da ya zama rayukan al’umma na salwanta, to ba wani abu mai alfanu da zai iya gudana. Don haka kamar yadda kasar Sin ta sha bayyanawa, ya wajaba kwamitin tsaron MDD, da sauran sassan masu ruwa da tsaki su tashi tsaye wajen sauke nauyin dake wuyansu, na wanzar da zaman lafiya, da tsaro a sassan kasa da kasa ta hanyar ingiza manufar dakatar da bude wuta, da warware rikici ta hanyar shawarwari.
Idan har manyan kasashen duniya masu fada a ji suka rungumi wannan kira na kasar Sin, suka samar da goyon bayan da ya dace, tabbas duniya za ta daidaita, kuma al’ummun duniya za su kai ga cimma kyakkyawan yanayin zamantakewa mai karko.