Tun bayan komawa sabon zagaye na tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin wakilan Sin da na Amurka a birnin Madrid na Sifaniya a karshen makon jiya, masharhanta da dama ke bayyana mahangarsu game da matsayar Sin dangane da zaman tattaunawar.
A mahangar da dama daga masu fashin baki, yayin zama na wannan karo ma kasar Sin za ta kara jaddada matsayinta na mai burin kare halastattun hakkokinta, da martaba tsarin cudanyar mabanbantan sassan duniya, tare da bukatar Amurka ta amince da gudanar da shawarwari bisa daidaito, da martaba juna, da dakile sabani, da karfafa hadin gwiwa, da hada hannu wajen bunkasa hada-hadar tattalin arziki ba tare da rufa-rufa ba.
Ko shakka babu alakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka ta cimma moriyar juna ce. Don haka ne ma karkashin kudurorin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, a baya tawagogin tattaunawa na Sin da Amurka, suka gudanar da zagaye uku na tattaunawa a Geneva, da Landan, da Stockholm, inda suka cimma sakamako mai gamsarwa da ya taka rawar gani wajen daidaita alakar kasashen biyu.
Tabbas, muhimmancin alakar cinikayya tsakanin Sin da Amurka ta zarge batun cimma gajiyarsu su kadai, domin kuwa hakan na shafar daidaiton tattalin arzikin duniya baki daya. A bangarenta, kasar Sin na ta kokarin sauke nauyin dake wuyanta a fannin warware sabani, da kaucewa fito-na-fito ta hanyar karfafa hadin gwiwa.
Baya ga kasar Sin, sauran sassan kasa da kasa ma suna nuna gamsuwa da nasarorin da ake samu, dangane da shawarwarin da sassan biyu ke gudanarwa. Suna kuma karfafa wa sassan biyu gwiwar ci gaba da shawarwari, ta yadda za su karfafa daidaito a fannin jagorancin hada-hadar cinikayya a matakin kasa da kasa.
Har kullum, Sin za ta ci gaba da martaba ka’idojin kare hakkokin kamfanoninta. Duba da cewa manhajar TikTok ta shafe tsawon shekaru tana aiki a Amurka, ta kuma samar da dumbin ayyukan yi ga tarin Amurkawa, tare da bayar da gudummawa ga tattalin arzikin kasar, ya kamata gwamnatin kasar ta baiwa manhajar damar cin gajiya daidai da sauran makamantanta dake kasar. Kamar dai ko da yaushe, burin Sin shi ne wanzar da daidaito da cimma moriyar bai daya tare da Amurka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp